An ayyana neman tsohon jami'in sojan ruwa? DHQ ta yi cikakken bayani

An ayyana neman tsohon jami'in sojan ruwa? DHQ ta yi cikakken bayani

  • Wani tsohon kwamandan rundunar sojan ruwa, Kunle Olawunmi, ya kasance cikin labarai bayan hirarsa ta kwanan nan a gidan talabijin na Channels
  • Hedkwatar tsaro ta yi bayanin yanayin da ke tattare da gayyatar da ta yi wa tsohon jami’in sojan ruwan
  • Gwamnatin tarayya ta sha shan suka daga 'yan kasar kan karuwar rashin tsaro a fadin kasar

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta musanta rahotannin da ke cewa ta ayyana neman tsohon kwamandan rundunar sojan ruwa, Kunle Olawunmi, ruwa a jallo kan kalaman da ya yi yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Hedikwatar tsaro (DHQ) ta bayyana rahoton a matsayin mara tushe.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An alanta neman tsohon sojan da yace gwamnati ta san masu daukar nauyin Boko Haram

An ayyana neman tsohon jami'in sojan ruwa? DHQ ta yi cikakken bayani
Hedkwatar tsaro ta ce ba ta ayyana neman tsohon jami'in sojan ruwa ba Hoto: Defence Headquarters Nigeria, Channels Television
Asali: Facebook

Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Benjamin Sawyerr, ya yi ikirarin cewa an gayyaci Olawunmi ne ta hanyar sakon tes don raba bayanan sirri da Sojojin.

DHQ ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

''Don Allah 'yan jarida. Akwai labarai na jaridar Sahara reporters cewa DIA ta ba da umarnin a kama Cdre Olawunmi rtd. Wannan karya ne kuma ba gaskiya bane. Za mu ba da sanarwa nan ba da jimawa ba.''

Manjo Sawyerr ya bayyana cewa an gayyaci babban jami'in sojan ruwa mai ritaya ne kawai don ya zo ya raba bayanan da za su taimaka wa sojoji wajen yakar 'yan tawaye da 'yan fashi.

Mai magana da yawun DHQ ya bayar da hujjar cewa gayyatar ba ta zama izinin kamawa ba, Leadership ta ruwaito.

Ya ce:

''Kungiyar leken asiri kamar dangi ne, wani daga DIA yana kallon babban jami'in yana magana kuma yanzu ya kira shi. ‘Oga idan kana da irin wannan bayanin zai yi kyau ka raba wa DIA. Don Allah, za ka iya zuwa ranar Talata ka raba tare da mu domin ta taimaka wa hukumomin tsaro su magance matsalar a kan lokaci. ’Shin hakan ya zama izinin kamawa? Gayyata ba kamawa bane.”

Kara karanta wannan

Hukumar DSS ta sammaci yan jaridar ChannelsTV kan hirar da sukayi da wani tsohon Soja

Kunle Olawunmi ya yi ikirarin cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun taba ambaton sunayen wasu mutanen da ke aiki a wannan gwamnati a matsayin masu daukar nauyin ta'addanci.

A wani labari na daban, majalisar dokokin jihar Filato ta nemi mazauna yankin da su kare kansu. Jihar ta fada cikin rikici a 'yan makonni biyu da suka gabata.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a Jos, babban birnin jihar Filato, a ranar Juma’a, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Hon. Dasun Philip Peter, ya ce tsarin tsaro na yau da kullun ba zai iya ba da tabbacin tsaro ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel