Obasanjo: Masu son ganin rabewar kasar nan makiyanta ne, za su ji kunya

Obasanjo: Masu son ganin rabewar kasar nan makiyanta ne, za su ji kunya

  • Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce duk wasu makiyan Najeriya masu mata fatan rabuwa ba za su ci nasara ba
  • A wata takarda wacce hadimin yada labaransa, Kehinde Akinyemi ya saki, ya yanko inda Obasanjo yake cewa sai ya fi sauki a bar Najeriya a dunkule akan a rabata
  • Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a wani taron kaddamar da wani Littafi “My Life and Times” wanda Sunday Mbang ya rubuta

Lagos - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Juma’a ya ce yawancin makiyan Najeriya wadanda suke fatan rabewar ta ba za su ci nasara ba, Daily Trust ta ruwaito.

A wata takarda wacce hadiminsa na harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya saki, ya ce Obasanjo ya ce kasancewar ‘yan Najeriya tare ya fi sauki a kan rabewarsu.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Mun taba yi wa mutum 76 jana’iza a lokaci guda, babu wanda ya ji labari inji Sultan

Obasanjo: Masu son ganin rabewar kasar nan makiyanta ne, za su ji kunya
Obasanjo: Masu son ganin rabewar kasar nan makiyanta ne, za su ji kunya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An ruwaito yadda yayi wannan jawabin yayin kaddamar da wani littafi mai suna “My Life and Times”, wanda Sunday Mbang ya rubuta.

An yi kaddamarwar ne a Admiralty Centre da ke Naval Dockyard, Victoria Island a jihar Legas.

An kaddamar da littafin ne don girmamawa ga Sunday Mbang, tsohon shugaban kungiyar Kiristoci na Najeriya.

Obasanjo yace “da yawan makiyan” wadanda suke son ganin Najeriya a rarrabe ba za su ci nasara ba.

Tsohon shugaban kasan ya yabawa Mbang a kan kokarinsa na ganin ya rike kyakkyawar alakarsu ta tsawon shekaru.

Ya bayyana shi a matsayin masoyin Najeriya.

Ya kamata mu girmama mai girma kuma mu koya daga Mbang, mu nuna cewa muna son shi kwarai kuma muna yaba masa dangane da yadda ya shugabanci jama’an kirista a kasar nan da duniya.

Kara karanta wannan

Kar 'yan Najeriya su tsorata da yawan 'yan Boko Haram da ke tuba, CDS Irabor

Kuma mu tabbatar masa da cewa duk abinda zai faru ba zai taba raba mu ba. Kuma za mu cigaba da yin ayyuka tukuru don samar da zaman lafiya, tsaro da cigaban kasar nan.
Na san wadannan ne abubuwan da kowannen mu yake fata a zuciyarsa. Muna so mu tabbatar muku da cewa Najeriya za ta cigaba da wanzuwa saboda ya fi mana sauki mu cigaba a tare a kan mu rabu.
Akwai mutane da dama, talakawa da masu kudi- wadanda makiyan Najeriya ne amma ba za su iya samun nasara ba, a cewar Obasanjo.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, a taron, gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Enmanuel shi ne shugaban taron.

Ya yaba wa tsohon shugaban kasar da kuma mai taron a kan yadda suka cigaba da tarayya a matsayin abokan juna har tsufarsu.

Zamfara: Ƴan bindiga sun sheƙe rai 1, sun tasa keyar 7 kan ƙin biyan haraji

Kara karanta wannan

Secondus: Abin da ya sa aka ga mun yi zuga, mun ziyarci tsohon Shugaban kasa Obasanjo

A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga sun sheke mutum 1 kuma sun tasa keyar mutum bakwai a kauyukan Dadah, Tukurawa da Gandamasu a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Premium Times ta ruwaito cewa, miyagun 'yan bindigan sun kai farmaki kauyukan a daren Alhamis sakamakon kin biyan haraji da mazauna kauyen suka yi wanda 'yan bindigan suka kallafa musu.

Zurmi tana daya daga cikin kananan hukumomi a jihar Zamfara da 'yan bindiga suka gallaba. Suna da iyakoki da karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel