Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

  • 'Yan bindiga sun kai mummunan hari kauyen Dan-Kumeji da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina
  • An tattaro cewa sun kashe mutane 11 tare da jikkata wasu shida a harin da suka kai da misalin karfe 11:30 na dare
  • Zuwa yanzu ba a ji ta bakin rundunar 'yan sandan jihar ba kan lamarin

Rahotanni sun kawo cewa ‘yan bindiga sun harbe akalla mazauna kauyen Dan-Kumeji da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina 11 har lahira.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mutane shida da suka samu raunuka a harin suna karbar magani a asibiti a yanzu haka.

Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina
Yan bindiga sun harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wani mazaunin garin, Abdulmumini Sani, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho, ya ce maharan sun afka wa kauyen da misalin karfe 11:30 na dare inda suka fara harbi ba kakkautawa, jaridar Thisday ta kuma ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: 'Yan Najeriya ba su cancanci wannan ba - Majalisar wakilai

Ya ce:

“Lokacin da mutanenmu suka gan su, sai suka fara gudu don tsira, ba tare da sanin cewa wasu daga cikin maharan sun yi kwanton bauna a wurare masu mahimmanci ba. Sai kawai suka fito suka fara harbin wadanda ke kokarin tserewa daga harin.”

Ya kara da cewa a safiyar yau Juma'a an kirga gawarwaki kusan 11 kuma ana ci gaba da shirye-shiryen binne gawarwakin da aka gano.

Kakakin ‘yan sanda a Katsina, SP Gambo Isah, bai tabbatar da faruwar lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

‘Yan bindiga sun karbi N68m da sababbin babura kafin su fito da ‘Yan Islamiyyan Tegina

A wani labarin, mun ji cewa sauran ‘daliban makarantar Islamiyyar Tanko Salihu da aka dauke a garin Tegina, jihar Neja, sun fito ne bayan an kara wa ‘yan bindiga kudi.

Kara karanta wannan

Gidaje 5 na hafsoshin soja 'yan bindiga suka balle a NDA Kaduna

Jaridar Daily Trust ta samu labari cewa sai da aka kara wa ‘yan bindigan kudin fansa bayan sun ki karbar Naira miliyan 50 da aka kai masu a baya.

‘Yanuwa da iyayen wadannan yara sun yi kokarin kara hada Naira miliyan 30 bayan sun biya Naira miliyan 20 domin a ceto yaran a watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel