Sojojin Amurka 13 suka rasa rayukansu a harin Bam da aka kai Afghanistan

Sojojin Amurka 13 suka rasa rayukansu a harin Bam da aka kai Afghanistan

  • Gwamnatin Amurka ta bayyana adadin jami'an da ta rasa sakamakon harin Bam a Afghanistan
  • Amurka na cigaba da kwasan yan kasarta da kuma wasu yan Afghanistan da suka taimaka mata
  • An baiwa Amurka zuwa ranar 31 ga Agusta ta gama kwasan duk wadanda zata kwasa

Amurka - Akalla dakarun Sojin Amurka 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin kunar bakin wake da ake zargin yan ta'addan ISIS suka kai tashar jirgin saman Afghanistan.

Shugaban rundunar Sojin Amurka dake kasashen waje, Kenneth "Frank" McKenzie, ya bayyana hakan a hira da manema labarai, CNN ta ruwaito.

Yace:

"Yau dai abubuwan takaici sun faru."

McKenzie yace yan kunar bakin wake biyu ne suka fara kai hari sannan kuma wasu yan bindiga suka bude wuta.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun sheƙe rai 1, sun tasa keyar 7 kan ƙin biyan haraji

Sojojin Amurka 12 suka rasa rayukansu a harin Bam da aka kai Afghanistan
Sojojin Amurka 12 suka rasa rayukansu a harin Bam da aka kai Afghanistan Hoto: edition.cnn.com
Asali: UGC

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya lashi takobin binciko wadanda suka aikata wannan ta'adi inda yan Amurka 13 suka mutu kuma 18 suka jikkata.

Ma'aikatar lafiyan Afghanistan ta bayyana cewa yan kasarta 60 suka mutu kuma akalla 140 suka jikkata, CNN ta samu ji.

Bama-bamai biyu sun tashi a kusa da filin jirgi a kasar Afghanistan

Bama-bamai biyu sun tashi a wajen tashar jirgin saman Hamid Karzai dake kasar Afghanistan yayinda jirage ke cigaba da kwasan yan kasar dake son komawa Amurka, Hukumar Sojin Amurka ta sanar da hakan.

Kakakin hedkwatar Sojin Amurka Pentagon, John Kirby, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki, rahoton Aljazeera.

Gwamnatin Amurka a farkon makon nan ta samu labarin leken asiri cewa wasu yan kunar bakin wake na shirin kai hari filin jirgin saman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel