Ya zama dole ku bayyana mana su wanene 'Unknown Gunmen', Sarkin Musulmi ya fada wa Hukumomin Tsaro

Ya zama dole ku bayyana mana su wanene 'Unknown Gunmen', Sarkin Musulmi ya fada wa Hukumomin Tsaro

  • Sarkin Musulmi ya bukaci hukumomin tsaro su bayyana su wanene 'unknown gunmen'
  • Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi wannan jawabin ne wurin taron NIREC a birnin tarayya Abuja
  • Muhammad Sa'ad Abubakar ya kuma bukaci jami'an tsaro su gaggauta daukan mataki kan malaman addini da ke tunzura mutane

FCT, Abuja - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar, ya bukaci hukumomin tsaro a Nigeria su bayyana ko su wanene 'unknown gunmen', ma'ana 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, rahoton Daily Trust.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja a wurin taron Majalisar Harkokin Addinai ta Nigeria, NIREC, na uku a cikin shekarar.

Ya zama dole ku bayyana mana su wanene 'Unknown Gunmen', Sarkin Musulmi ya fada wa Hukumomin Tsaro
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Mun taba yi wa mutum 76 jana’iza a lokaci guda, babu wanda ya ji labari inji Sultan

Daily Trust ta ruwaito cewa sarkin, wanda kuma shine shugaban NIREC, ya ce lamarin rashin tsaro a kasar ya kai wani matsayin damuwa matuka.

Ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu mutanen da ba a sani ba za su kashe mutane da dama kuma babu wani mataki da aka dauka na hukunta su.

Ya ce:

"Dukkan mu mun damu bisa rashin tsaro a kasar nan. Abin da na ke cewa shine abubuwa kara tabarbarewa suke yi kuma zan cigaba da fadan hakan.
"Ta yaya za a ce ba a san su ba? Mutanen da ba a sani ba za su kashe mutane da dama kuma babu abin da aka yi? Ina hukumomin leken asirin mu? Ba mu da jami'an leken asiri ne da za su rika binciken sirri ko gano wani bata gari tun kafin ya aikata laifi? Ni soja ne kuma na san abin da na ke fada."

Sarkin Musulmi ya soki shugabannin addini masu tunzura mabiyansu

Kara karanta wannan

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

Ya kuma soki wasu shugabannin addini da ke tunzura mabiyansu.

Ya cigaba da cewa:

"Dayan shugaban na NIREC, (Shugaban CAN Ayokunle) ya yi magana game da wani malamin addinin musulunci. Ban taba ji ba sai da na ga bidiyon, kuma na san wani a Plateau wanda ya yi mummunan bidiyo yana kira ga matasa su tashi su halaka musulmi, yana nan ya bazu a soshiyal midiya.
"Me hukumomin tsaro ke yi? Ba za su gayyaci mutanen nan ba su gano mene suke nufi? Babu wanda ya fi karfin doka, musulmi ko kirista, ba zai yiwu ka rika tunzura mutane ba su yi kisa."

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

A wani labarin daban, Kungiyar kirista ta Nigeria, CAN, a Jos, babban birnin jihar Plateau ta roki shugabannin musulmi da na kirista su dena tunzura mutane suna miyagun ayyuka, Peoples Gazette ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos

A cewar sanarwar da ta fitar a garin Jos a ranar Laraba mai dauke da sa hannun shugaban CAN, Polycarp Gana da satare Ezekiel Noam, kungiyar ta kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a Yalwan Zangam.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka garin a daren ranar Talata sun kashe mutane masu yawa sannan suka kona gidaje da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel