Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

  • Rahoto daga jihar Neja na bayyana cewa, an sako daliban makarantar Islamiyya da aka sace
  • A halin yanzu an ce suna kan hanyarsu da zuwa birnin Minna daga ta hanyar Kagara daga Birnin Gwari
  • Wannan na zuwa ne bayan sun shafe kwanaki sama da 88 a hannun 'yan bindigan da suka sace su

Neja - Sama da dalibai 70 'yan bindiaga suka sako na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda aka yi garkuwa da su kwanaki 88 da suka gabata, PR Nigeria ta ruwaito.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an sace daliban ne a harabar makarantar Islamiyyar dake Tegina a watan Yunin 2021.

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace
Daliban Tegina | Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar PRNigeria cewa daliban na kan hanyarsu ta zuwa Minna akan hanyar Kagara daga Birnin Gwari.

An tsare daliban Islamiyyar na tsawon kwanaki 88 da awanni 11 gwargwadon lokacin da suka shafe a hannun 'yan bindigan kenan.

Kara karanta wannan

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon da mutum 50, sun hallaka mutum 4 a Maradun

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Litinin 23 ga watan Agusta ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka mutum hudu tare da yin awon gaba da wasu mutum 50 a garin Goran Namaye da ke karamar hukumar Maradun.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, Muhammad Shehu, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Muhammad Shehu, ya ce maharan, wadanda suka zo da yawansu, sun mamaye garin da tsakar daren ranar Lahadi, inda suka kashe mutum hudu tare da sace wasu 50.

An kame wani saurayi da ya dirkawa budurwa ciki, ya kashe, ya binne ta a Adamawa

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta gurfanar da wani dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Mubi, Mumuni Abubakar, bisa zargin kashe budurwarsa mai juna biyu, Franca Elisha, tare da binne gawarta a cikin rami mara zurfi.

Rundunar ta kuma gurfanar da wasu abokansa biyu, Huzaifa Shuaibu da Rabiu Adamu, saboda rawar da suka taka dumu-dumu a lamarin, Punch ta ruwaito.

Franca Elisha, dalibar Diploma a Sashen Kimiyyar Laburare a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya dake Mubi, an binne ta a cikin rami mara zurfi bayan kokarin zubar da ciki da ta yi ya faskara.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, ya ce korafin da iyayen marigayiyar suka yi game da inda take ya kai ga binciken da ya gano yanayin da ke tattare da mutuwar ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel