Hukumar DSS ta sammaci yan jaridar ChannelsTV kan hirar da sukayi da wani tsohon Soja

Hukumar DSS ta sammaci yan jaridar ChannelsTV kan hirar da sukayi da wani tsohon Soja

  • Gwamnati tarayya ta sammaci yan jarida zuwa Abuja
  • Wannan ya biyo bayan wasikar tuhumar da hukumar NBC ta aikewa Channels
  • Gwamnati na tuhumar ChannelsTV da yunkurin tayar da tarzoma a kasa

Rahotanni na nuna cewa hukumar DSS ta sammaci wasu yan jaridar gidan talabijin ChannelsTV dake Legas kan hirar da sukayi da wani tsohon Soja mai suna, Kunle Olawunmi.

A cewar Arise News, daya daga cikin lauyoyin Channels TV na tare da yan jaridan dake hanyarsu ta zuwa Abuja yanzu haka.

Wani hira yan jaridan sukayi?

A ranar Talata, tsohon Sojan Ruwa, Commodore Kunle Olawunmi, a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta san wadanda ke daukan nauyin yan ta'addan Boko Haram da suka addabi kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta san masu daukan nauyin yan Boko Haram, wasu gwamnoni ne yanzu: Tsohon Jami'in Soja

Ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida a shirin Sunrise Daily na ChannelsTV.

Olawunmi yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Su (gwamnati) sun sani. A Afrilun shekarar nan, gwamnati ta ce ta damke yan kasuwar canji 400 dake daukan nauyin yan Boko Haram. Haka suka fada mana."

Hukumar DSS ta sammaci yan jaridar ChannelsTV kan hirar da sukayi da wani tsohon Soja
Hukumar DSS ta sammaci yan jaridar ChannelsTV kan hirar da sukayi da wani tsohon Soja Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

NBC Ta Tuhumi Channels TV Kan Tattaunawa da Gwamna Ortom

A bangare guda, hukumar kula da kafafen watsa labarai ta ƙasa (NBC), ta tuhumi Channels tv kan maganganun da Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, ya yi a shirinta na Sunrise daily ranar Talata.

Hukumar NBC ta bayyana hakane a wata takarda da ta aike wa kafar watsa labaran, kamar yadda punch ta ruwaito.

Takardar tana ɗauke da kwanan watan 24 ga watan Agusta, kuma shugaban hukumar NBC, Balarabe Ilelah, ya saka hannu.

Wasu maganganu Ortom ya yi?

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gida: Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Matakin da Ta Dauka Bayan Kotu Ta Dakatar da Secondus

Ortom, wanda ya bayyana a cikin shirin, yace:

"Shugaban ƙasa na sakani tunanin ko abinda ake faɗa kansa cewa yana da wata ɓoyayyar manufa ga ƙasar nan gaskiya ne."
"Saboda komai ya fito fili yana son maida ƙasar nan ta fulani kuma ba shine bafullatani na farko da ya shugabanci kasar nan ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel