Labari Da Duminsa: Rikicin Shugabancin PDP Ya Ƙare, an Nada Sabon Shugaba Na Kasa

Labari Da Duminsa: Rikicin Shugabancin PDP Ya Ƙare, an Nada Sabon Shugaba Na Kasa

  • Babban jam'iyyar hamayya a Nigeria ta PDP ta kawo karshen rikicin shugabanci da ya taso bayan kotu ta dakatar da Uche Secondus
  • Bayan dakatar da Secondus, mutane biyu sun yi ikirarin cewa sune shugabannin jam'iyyar wadda hakan ya janyo rikici
  • Sai dai daga karshe, mahukunta a jam'iyyar sun yi taro a ranar Alhamis sun amince da nadin Yemi Akinwonmi a matsayin mukadashin shugaba

FCT, Abuja - Bayan kwanaki biyu ana dambarwa kan shugabancin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, an nada mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa (kudu), Yemi Akinwonmi a matsayin mukadashin shugaba, The Cable ta ruwaito.

Mai magana da yawun jam'iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ne ya sanar da hakan bayan taron sirri da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta yi a ranar Alhamis a Abuja, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Liyafa Ta Cigaba, Tsohon Shugbaan Kasa Jonathan Ya Samu Babban Mukami a Kasar Waje

Labari Da Duminsa: Rikicin Shugabancin PDP Ya Ƙare, an Nada Sabon Shugaba Na Kasa
Yemi Akinwonmi, sabon mukadashin shugaban PDP na kasa. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Akinwonmi zai maye gurbin shugaban jam'iyyar na kasa, Uche Secondus, wanda ranar Litinin wata babban kotun jihar Rivers ta hana shi cigaba da zama shugaban PDP na kasa.

Ya tabbatar da sauya taron kwamitin masu gudanarwa na jam'iyyar wato NEC zuwa ranar Asabar.

Mr Ologbondiyan ya shaidawa manema labarai cewa:

"A madadin jam'iyyar mu, ina iya cewa mun magance matsalar da ta taso, kuma kaman yadda kuka gani, mun taho mun gabatar da kudiiri kuma an amince da Elder Yemi Akinwonmi a matsayin mukadashin shugaban gagarumar jam'iyyar mu."
"Za ku yi mamakin sanin cewa hakan na cikin kudin tsarin jam'iyyar mu."
"Za mu yi taron NWC din mu a gobe gabanin shirya taron kwamitin shugabannin jam'iyya da za a yi a ranar Asabar."

Akinwonmi ya fara aiki a matsayin shugaban rikon kwarya na jam'iyyar bayan umurnin da kotu ta bayar na tsige Uche Secondus a matsayin shugaban jam'iyya.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Bama-bamai biyu sun tashi a kusa da filin jirgi a kasar Afghanistan

Kotu ta dakatar da Secondus daga ɗaukar kansa Shugaba

A ranar Litinin ne kotun na jihar Rivers ta yanke hukuncin hana Secondus cigaba da kasancewa shugaban jam'iyyar na kasa.

Mai shari'a O. Gbasam, ya tumbuke Secondus daga matsayin shugaban PDP yayin da yake yanke hukunci kan karar da jiga-jigan PDP suka shigar a kansa.

Wadanda suka shigar da karar sun hada da, Ibeawuchi Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da kuma Umezirike Onucha.

Wani sashin jawabin Alkalin yace:

"Kotu da bada umarnin hana wanda ake kara daga bayyana kanshi a matsayin shugaba ko kuma gudanar da ayyukan shugaba."
"Hakanan kotu ta umarci hana wanda ake kara kira, halarta ko jagorantar wani taro ko shiga wani kwamiti a matakin gunduuma, karamar hukuma ko jiha.
"Kuma an hana wanda ake kara daga shirya gangamin taron gundumomi, kananan hukumomi ko jiha yayin da aka dakatar da shi daga kasancewa ɗan jam'iyya."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel