Da duminsa: Tattalin arzikin Najeriya ya karu da 5.01% a cikin wata 3 kacal

Da duminsa: Tattalin arzikin Najeriya ya karu da 5.01% a cikin wata 3 kacal

  • Labari mai dadi dake bayyana shine na habakar tattalin arzikin Najeriya da kashi 5.01 a cikin watanni uku
  • Kamar yadda rahoton NBS ya nuna, an samu wannan nasarar ne bayan dawowar harkokin kasuwanci bayan korona
  • Kasar Najeriya ta fada kwata ne tun bayan da kasar ta wulla cikin matsalar karayar arziki a cikin shekarar 2016

Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 5.01 a tsakanin watan Afirilu zuwa watan Yuni na 2021 daga kashi 0.51 da aka samu a watanni uku na farkon shekarar nan.

Rahoton daukacin kayan aiki da kasar nan ta samar a na watanni uku wanda NBS ta fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa wannan cigaban na kashi 5.01% shine mafi girma da aka taba samu tun daga karshen shekarar 2014, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: 'Yan Najeriya ba su cancanci wannan ba - Majalisar wakilai

Da duminsa: Tattalin arzikin Najeriya ya karu da 5.01% a cikin wata 3 kacal
Da duminsa: Tattalin arzikin Najeriya ya karu da 5.01% a cikin wata 3 kacal. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wannan habakar tattalin arzikin ya fi na wancan shekarar 2020 da ta gabata tare da ta watanni uku na farko na wannan shekarar da aka gani.

Daily Trust ta ruwaito cewa, rahoton karuwar tattalin arzikin labari ne mai dadi kuma alamun nasarar ne da ya bayyana shekarar 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce wannan alamu ne na dawowar kasuwanci da al'amuran tattalin arziki bayan aukuwar muguwar annobar korona.

NBS ta kara da bayanin cewa:

Farfadowar tattalin arzikin kasar nan da ya fara daga karshen 2020, tare da dawowar al'amuran kasuwanci a gida Najeriya da duniya baki daya, shine silar cigaban da ake gani.

Kiyasi kan rahoton ya nuna cewa bangaren da ba na man fetur ba ya samar da kashi 6.74 inda sauran kashin an samo shi ne daga kasuwanci, yada labarai da sadarwa, sufuri da sauransu kamar yadda rahoton ya sanar.

Kara karanta wannan

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

Tattalin arzikin Najeriya ya fada wani hali tun a shekarar 2016 yayin da kasar ta fada matsalar karayar tattalin arziki.

Ku binciki hanyar samun kwastomomin ku, EFCC ga bankuna

A wani labari na daban, shugaban EFCC ya umarci bankuna a kan bincike hanyoyin samun kudaden abokan harkokin su.

Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC ya furta hakan a ranar Talata lokacin da ACAEBIN ya kai masa ziyara har Abuja.

Kamar yadda The Cable ta wallafa, Bawa ya ce akwai abokan huldar banki da makudan kudade za su shiga asusunsu cikin watanni biyu da bude asusun bankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel