Mutum 16 Sun Mutu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Ragargaji Mayakan Boko Haram 50 a Nijar

Mutum 16 Sun Mutu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Ragargaji Mayakan Boko Haram 50 a Nijar

  • Mayakan Boko Haram sun kai hari kudu maso gabashin Nijar dake fama da hare-haren masu ikirarin jihadi
  • Ministan tsaron kasar yace an kashe sojoji 16 tare da jikkata wasu mutum 9 yayin harin na ranar Talata
  • Ministan yace dakarun sojin sun samu nasarar hallaka yan ta'addan kusan 50 a fafatawar

Niger Republic - Wani hari da ɗaruruwan mayakan Boko Haram suka kai a wani gari dake fama da matsalar yan jihadi a Nijar, ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 16, wasu 9 suka jikkata, kamar yadda channesl tv ta ruwaito.

Ministan tsaron kasar, Alkassoum Indatou, shine ya shaidawa AFP haka ranar Laraba.

A harin na ranar Talata, ministan yace:

"Daruruwan mayakan Boko Haram sun kai harin sansanin jami'an tsaron mu na Baroua, yankin Diffa, maharan sun fito ne daga tafkin Chadi."

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Dakarun Sojoji Sun Yi Artabu da Mayakan Boko Haram a Yobe

"Sojojin Nijar sun hallaka yan ta'adda kusan 50, sannan sun kwato manyan makamai da alburusai da yawan gaske."
Tutar kasar Nijar
Mutum 16 Sun Mutu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Ragargaji Mayakan Boko Haram 50 a Nijar Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane sun fara komawa garuruwansu

Kusan mutum 6,000 sun koma gidajen su dake yankin Baroua a watan Yuni na wannan shekarar tun bayan tserewarsu saboda harin masu ikirarin jihadi a 2015.

Hukumomin sun bayyana cewa kauyuka 19 kamar Baroua, inda sama da mutum 26,000 suka dawo kwanan nan, suna karkashin tsatsauran tsaro, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

Duk da gwamnan Diffa, Issa Lemine, ya yaba da cigaban da ake samu a ɓangaren tsaro, ya kuma nuna jin daɗinsa da marhabun ga masu dawowa asalin gidajensu.

Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda suka guje wa garuruwansu saboda matsalar tsaro, suna rayuwa ne a wasu kauyuka masu tsaro a yankin.

Wasu yan Najeriya suna jihar Diffa

Kara karanta wannan

Afghanistan: Wata kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban, ta harba makami

Bugu da kari, kimanin mutane 300,000 da aka raba da muhallansu a Nijar da makociyarta Najeriya sun samu matsuguni a jihar Diffa, a cewar UN.

A farkon wannan watan ne gwamnatin Nijar ta bayyana cewa zata gina sansanin sojojin sama a yankin domin kara karfin yakin da take da masu ikirarin jihadi.

A wani labarin kuma Shugaban Jam'iyyar PDP, Adegbola Dominic, Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Shugaban babbar jam'iyyar adawa PDP, reshen jihar Lagos, Adegbola Dominic, ya kwanta dama.

Kakakin jam'iyyar na jihar, Taofeeq Gani, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Yace za'a sakko da tutocin PDP dake faɗin jihar Lagos zuwa rabi domin nuna alhinin mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel