Rikici ya barke tsakanin yan Boko Haram kan mika wuya, sun kashe juna 27

Rikici ya barke tsakanin yan Boko Haram kan mika wuya, sun kashe juna 27

  • Rikici ya barke tsakanin yan Boko Haram da ISWAP yayinda wasu ke kokarin mika wuya
  • An kashe akalla mutum 27 a musayar wuta da suka tsakaninsu
  • Yan Boko Haram kwanakin nan na mika wuya ga Sojoji

Borno - Yan ta'addan Boko Haram da ISWAP sun karkashe juna yayin rikicin da ya barke tsakaninsu a Arewacin Abadam, jihar Borno lokacin da wasu ke kokarin mika wuya.

PRNigeria ta ruwaito cewa wasu yan Boko Haram da suka shirya mika wuya sun fuskanci kalubale wajen yan ta'addan ISWAP da sukayi kokarin hanasu mika wuya.

Bangarorin biyu sun yi musayar wuta ne a unguwar Gusuriya dake garin Dumbawa.

Yan Boko Haram suna kan hanyarsu ta zuwa wajen rundunar Sojin hadaka ta MNJTF ne a iyakan Nijar ranar Lahadi, 22 ga Agusta, 2021 lokacin da aka kai musu hari.

Kara karanta wannan

Afghanistan: Wata kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban, ta harba makami

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa kwamandojin ISWAP sun nuna bacin ransu kan yadda yan Boko Haram ke mika wuya kuma hakan ya sa suka kafa dokar kisa ga duka wanda aka kama yana kokarin mika wuya.

Majiyar tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wani mai suna Abba-Kaka, gwamnan Tumbumma, wanda ke jagorancin Marte, Abadam, Kukawa da Magumeri, ne ya jagoranci harin inda aka kwashe awanni ana musayar wuta kuma aka kashe mutum 25. cikin har da kwamandoji uku, yayinda sauran suka arce da iyalansu."

Rikici ya barke tsakanin yan Boko Haram kan mika wuya, sun kashe juna 27
Rikici ya barke tsakanin yan Boko Haram kan mika wuya, sun kashe juna 27 Hoto: HumAngle
Asali: UGC

Me ya haddasa rabuwar kai tsakanin ISWAP da Boko Haram?

Wata majiyar daban ta bayyanawa PRNigeria cewa rabuwar kan dake tsakanin bangarorin biyu ya sake munana ne lokacin da aka kashe wasu yan ta'addan Boko Haram kan wasu laifukan da basu taka kara sun karya ba, da kuma kin basu mukamai manya.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Na Tsallake Harin Yan Boko Haram Sama da 50, Gwamna Zulum

A cewar majiyar:

"An kaskantar da wasu manyan Kwamandoji da Amirai karkashin Shekau bayan sun yi mubaya'a ga ISWAP."
"Wasu kwamandojin Boko Haram da mabiyansu sun fara shirin fito-na-fito da ISWAP t hanyar hada kai da Bakura da Krimima da suka dade suna yakan ISWAP a Lelewa, Duwa, Wallal da Hauwa Bulumwa a jamhuriyyar Nijar."

Rundunar sojojin Najeriya ta damke mai yi wa Boko Haram safarar taki a Yobe

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ta cafke wani Yusuf Saleh, wanda ake zargi da bai wa mayakan Boko Haram safarar takin zamani.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, daga daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, ya ce dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun cafke wanda ake zargin a kauyen Bayamari da ke karamar hukumar Geidam ta jihar Yobe.

Nwachukwu ya kara da cewa sojojin da ke sa ido sun damke wanda ake zargin da buhuhunan taki 38 (50kg) bayan samun bayanai.

Kara karanta wannan

Jami'an MNJTF sun sheke 'yan ta'adda 4, sun kwace miyagun makamai a Borno

Asali: Legit.ng

Online view pixel