Da Ɗumi-Ɗumi: Sabon harin Jihar Benue ya yi ajalin rayukan mutane 8

Da Ɗumi-Ɗumi: Sabon harin Jihar Benue ya yi ajalin rayukan mutane 8

  • A kalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu a wuraren Yelewta dake karamar hukumar Guma a jihar Binuwai
  • Ganau sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce ya faru ne ana dab da 'yan kasuwa za su rufe shagunan
  • Tuni kwamishinan 'yan sandan jihar ya garzaya har wurin 'yan uwan mamatan don ta'aziyya

Benue - A kalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu a garin Yelewta ta karamar hukumar Guma da ke jihar Binuwai.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ganau sun tabbatar da yadda lamarin ya auku daidai da 'yan kasuwa suna rufe shagunan su.

Shugaban karamar hukumar Guma, Celeb Aba ya sanar da manema labarai a Makurdi ta waya cewa an sheke wadanda lamarin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Da duminsa: Sabon harin jihar Benue yayi ajalin rayuka 8
Da duminsa: Sabon harin jihar Benue yayi ajalin rayuka 8
Asali: Original

Daily Trust ta wallafa cewa, Aba ya ce a ranar kasuwar Yelewta lokacin da mutane suka kusa rufe shagunan su kawai suka fara jin harbe-harben bindigogi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Take anan aka sheke mutane 8

Ranar kasuwa ce lokacin mutane suna tsaka da kasuwancin su kawai sai ga 'yan bindiga sun bayyana suna ta harbe-harbe ko ta ina. Daga karshe aka ga gawar mutane 8, sun yi garkuwa da mutum daya don har yanzu ba a gan shi ba," a cewarsa.

Shugaban karamar hukumar ya kara da bayyana yadda aka garzaya da wadanda suka samu raunuka asibiti don kulawa da lafiyarsu.

Anene ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Akingbola Olatunji ya kai ziyara don ta'aziyya ga 'yan uwa da abokan arzikin mamatan.

Ya tabbatar wa da mutanen Yelewta cewa jami'ansa za su tabbatar da sun samar da isasshen tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

An kashe mutane masu yawa, an yi ƙone-ƙone yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos

A wani labari na daban, an ruwaito cewa an kashe mutane da dama a garin Yelwan Zangam da ke karamar hukumar Jos ta Arewa na Jihar Plateau. Daily Trust ta ruwaito cewa an kuma kone gidaje masu yawa yayin harin.

Wannan na zuwa ne kimanin sati daya bayan kashe matafiya 27 a hanyar Gaba-biyu-Rukuba a karamar hukumar Jos din ta Arewa.

Yakubu Bagudu, wani mazaunin yankin ya tabbatarwa Daily Trust afkuwar wannan harin a safiyar ranar Laraba. Ya ce an kashe kimanin mutane 30, ya kara da cewa an turo jami'an tsaro zuwa yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel