Kar 'yan Najeriya su tsorata da yawan 'yan Boko Haram da ke tuba, CDS Irabor

Kar 'yan Najeriya su tsorata da yawan 'yan Boko Haram da ke tuba, CDS Irabor

  • CDS, Leo Irabor ya shawarci ‘yan Najeriya da su cire tsoro bisa yadda suka ga mayakan Boko Haram suna ta zubar da makamansu
  • Irabor ya bayar da wannan shawarar ne a wata takarda da Darektan yada labaran sojoji ya saki a ranar Talata a jihar Adamawa
  • Ya bayyana farin cikinsa game da yadda mutanen arewa maso gabas suke bai wa rundunonin sojoji hadin kai mai yawan gaske

Adamawa - Shugaban ma'aikatan tsaro, Leo Irabor ya kwantar wa da ‘yan Najeriya hankali sannan ya bayar da shawarwari a kan yadda ya lura suna matukar sanya tsoron tubabbun mayakan Boko Haram a zuciyoyinsu.

Daily Nigerian ta wallafa cewa, Irabor ya bayar da shawarar ne a wata takarda da darektan labaran soji, Manjo janar Benjamin Sawyer ya saki bayan wata tattaunawa da manyan sojojin kasar nan masu murabus na arewa maso gabas suka yi da CDS din.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi zafi: Dole mu nemo tsoffin sojoji don a yaki ta'addanci, inji CDS

Kar 'yan Najeriya su tsorata da yawan 'yan Boko Haram dake tuba, CDS Irabor
Kar 'yan Najeriya su tsorata da yawan 'yan Boko Haram dake tuba, CDS Irabor. Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Irabor ya mika godiya ga jama'ar arewa maso gabas

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sun tattauna a ranar Talata ne a Yola. Irabor ya mika godiyarsa ga mutanen arewa maso gabas a kan hadin kan da suke bai wa sojoji.

Janar Irabor ya ce maganin matsalar tsaro a arewa maso gabas yana hannun mutanen yankin, kuma ya yi imani da cewa wata rana za a samu canji.
Dangane da tsoron da ya shiga zukatan ‘yan Najeriya a kan yadda mayakan Boko Haram da na ISWAP suke ta zubar da makamansu, ina so ‘yan Najeriya su yi imani da mu kan cewa za mu yi iyakar kokarin mu wurin ganin jami’an tsaro sun gyara tubabbun ‘yan Boko Haram din,” kamar yadda Irabor yace.

Sojoji zasu yi iyakar kokarinsu wurin taimakon arewa maso gabas

Kara karanta wannan

Ku daina miyagun kalamai game da tubabbun ƴan Boko Haram, ku yi musu zaton alheri, FG

A cewarsa, sojoji za su yi iya kokarinsu na ganin sun taimaka wa yankin nan, ba za su taba barin wani rashin tsaro ya kara barkewa ba.

CDS ya umarci sojoji a kan su zage kuma su daura damarar ganin sun kawo gyara a harkar tsaro.

Abinda ya fi bayyana shi ne yadda AFN suke kokarin dawo da arewa maso gabas cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali kamar yadda da take,” a cewar CDS.

Ya bayyana harin da ‘yan bindiga suka kai NDA a matsayin ta’addanci.

Ku daina miyagun kalamai game da tubabbun ƴan Boko Haram, ku yi musu zaton alheri, FG

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ja kunnen ‘yan Najeriya a kan yadda suke yawo da labaran karya dangane da tubabbun mayakan Boko Haram.

Vanguard ta ruwaito yadda ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da NAN ta yi dashi a ranar Juma’a a birnin Washington.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

An samu rahotanni a kan dubannin ‘yan Boko Haram da iyalansu suka yi mubaya’a ga sojojin Najeriya kuma suka mika wuyansu a Konduga, Bama da Mafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel