Da duminsa: Bayan kisan mutune, Gwamnan Plateau ya sake kakaba dokar ta baci ba dare ba rana

Da duminsa: Bayan kisan mutune, Gwamnan Plateau ya sake kakaba dokar ta baci ba dare ba rana

  • An kashe mutane masu yawa, an yi ƙone-ƙone yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos Karo na biyu, gwamna Lalong ya sanye dokar hana fita a jiharsa
  • Wannan karo wasu sun kai farmaki kan yan garin Yelwa Zangam kuma suka kashesu
  • Gwamnan ya yi kira ga jama'an gari sun kwantar da hankulansu komai zai daidaita

Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong, ya sake saka dokar ta baci a karamar hukumar Jos ta Arewa sakamakon kisan mutune da kone-kone a garin Yelwa Zangam.

Mun kawo muku rahoton cewa wasu yan bindiga sun kai hari garin Yelwa Zangam inda akalla mutum 30 suka rasa rayukansu.

Sakataren yada labaran gwamnan, Makut Simon Macham, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

Yace dokar za ta fara aiki ne daga karfe 4 na yamma har zuwa lokacin da hali yayi.

Makut yace:

"A cewar Gwamna Simon Lalong, dokar ta bacin awa 24 zata fara aiki daga karfe 4 na yamma, yau Laraba, 25 ga Agusta, 2021 har sai lokacin da hali yayi."
"Mun dauki wannan mataki ne sakamakon hadarin da rayukan mutane da dukiyoyinsu ke ciki a karamar hukumar."
"Wannan zai bawa jami'an tsaro daman tura dakaru wajen domin kwantar da kuran da neman wadanda suka kai harin."

Da duminsa: Bayan kisan mutune, Gwamna ya sake kakaba dokar ta baci ba dare ba rana
Da duminsa: Bayan kisan mutune, Gwamnan Plateau ya sake kakaba dokar ta baci ba dare ba rana Hoto: ChannelsTV
Asali: Facebook

An kashe mutane masu yawa, an yi ƙone-ƙone yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos

An ruwaito cewa an kashe mutane da dama a garin Yelwan Zangam da ke karamar hukumar Jos ta Arewa na Jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Gwamnan jihar ya tabbatar da wannan hari kuma yayi Allah wadai da wannan hari.

Ya yi kira ga al'ummar garin su kwantar da hankulansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel