Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

  • Janar Abdulsalami, ya yi kira ga sake dabara wajen magance matsalolin tsaron Najeriya
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da 'yan jarida a wata ganawa dasu a jihar Neja
  • Hakazalika, ya bukaci 'yan jarida da su kasance masu ba da rahotannin gaskiya a kowane lokaci

Jihar Neja - Tsohon shugaban kasa, Janar Abdusalami Abubakar (mai ritaya) ya yi kira da a sake dabara don kokarin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasar nan, inda ya koka da yadda lamarin ya zama abin damuwa matuka.

Da yake magana lokacin da manyan jami’an kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Neja suka kai masa ziyara a gidansa na Hilltop da ke Minna, ya ce abin damuwa ne cewa mutane ba za su iya bacci ba tare da tsammanin harin tsageru a kowace rana ba.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi zafi: Dole mu nemo tsoffin sojoji don a yaki ta'addanci, inji CDS

Janar Abdulsalami: Ya kamata a zage damtse a nemo mafita ga tsaron kasar nan
Janar Abdulsalami Abubakar | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito Abdulsalami yana cewa:

“Idan kana son yin tafiya daga wannan wuri zuwa wani, za ka fara shiga damuwa; muna addu’ar Allah ya kawo mafita domin ya yi alkawarin cewa babu wata wahala da ba ta da mafita.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kamata 'yan jarida su kasance masu da'a kan aikinsu

Abdulsalami ya bukaci 'yan jarida da suka kasance masu bayar da rahoto bisa da'a na aiki, kuma su guji kuskuren sanar da jama'a ba daidai ba musamman kan al'amuran tsaro.

Shugaban Majalisar NUJ, Abu Nmodu, ya ce sun kai ziyarar ne don fahimtar juna da neman shawarar tsohon shugaban don inganta sana’ar yada labarai.

A wani labarin mai kama da haka, Kwamishinan 'yan sanda na jihar Neja, Monday Bala Kuryas, ya kalubalanci' yan jarida da su guji yada rahotannin da ke iya tayar da hankali da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

CP Kuryas ya bayyana harkar kafafen yada labarai a matsayin kwakkwarar sana’a da ke tafiya akan tafarkin gaskiya, hakikanin gaskiya, don haka, ya tabbatar wa kungiyar da membobinta goyon baya.

Lamari ya yi zafi: Dole mu nemo tsoffin sojoji don a yaki ta'addanci, inji CDS

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Lucky Irabor, ya ce Sojojin Najeriya za su nemo jami’an sojojin da suka yi ritaya don magance matsalar rashin tsaro a yankin arewa maso gabas.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata 24 ga watan Agusta a wani zaman tattaunawa na kwana daya tare da manyan jami’an da suka yi ritaya daga shiyyar arewa maso gabas da aka gudanar a runduna ta 23 da ke Yola, jihar Adamawa.

A jawaban da ya gabatar, Irabor ya ce:

“Yana daga cikin dalilin da ya sa nake nan tare da tawaga ta, don damawa da manyan abokan aikinmu da suka yi ritaya domin neman cikakkiyar mafita game da yadda za a kawo karshen rashin tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Farfesa Aminu Dorayi: Bakanon da ya tuko motarsa daga Landan har zuwa Kano

"Mun yi imanin cewa yayin da muke damawa da su, za su kasance a shirye don bude mana hanya a wuraren da za su inganta tsaro, kuma za su iya gaya mana wuraren da kuskuren mu ne don mu yi gyara."

Mambobin majalisa sun fashe da kuka saboda yawaitar harin 'yan bindiga

A wani labarin, 'Yan majalisar dokokin jihar Katsina biyu, a ranar Litinin, sun fashe da kuka a bayyane bisa yawan hare-haren da aka kai kwanan nan a cikin al'ummomin jihar ta Katsina, The Cable ta ruwaito.

Da yake magana ranar Litinin a zauren majalisar wanda kakakin majalisar Tasi’u Maigari ke jagoranta, Shehu Dalhatu-Tafoki, mataimakin kakakin majalisar, ya gabatar da wani kudiri na “mahimmantar da bukatar jama’a cikin gaggawa” kan matakin rashin tsaro a jihar.

A cewar Dalhatu-Tafoki, mamba mai wakiltar mazabar Faskari, duk da kokarin gwamnatin tarayya da na jihohi, da hukumomin tsaro, har yanzu al’ummomi na fuskantar hare-hare.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Asali: Legit.ng

Online view pixel