Gwamna Lalong Ya Gana da Shugaba Buhari Kan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai a Jos, Buhari Ya Yi Alkawari

Gwamna Lalong Ya Gana da Shugaba Buhari Kan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai a Jos, Buhari Ya Yi Alkawari

  • Gwamnan Filato, Simon Lalong, ya yiwa shugaba Buhari bayani game da halin da ake ciki a Filato
  • Rahotanni sun bayyana cewa ana kara samun rikice-rikice a jihar tun bayan kisan matafiya da wasu bara gurbi suka yi a Jos
  • Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa zata taimakawa waɗanda lamarin ya shafa

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya saurari bayanai kan kisan gillan da a kaiwa musulmi a Jos a rikicin da suka biyo baya daga gwamnan Filato, Simon Lalong, ranar Talata.

Bayan sauraron inda aka kwana game da lamarin, shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya ta hanyar ma'aikatar jin kai da walwala, zata tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa.

Vanguard ta ruwaito cewa gwamna Lalong ya yi barazanar hukunta duk wanda ke da hannu a tada rikici a lungu da sako na jihar Filato.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Shugaba Buhari da gwamnan Filato, Simon Lalong a fadar shugaban kasa
Gwamna Lalong Ya Gana da Shugaba Buhari Kan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai a Jos, Buhari Ya Yi Alkawari Hoto: Buhari Sallau FB Fage
Asali: Facebook

Zaman lafiya ya samu a Filato

Da yake jawabi ga manema labarai na gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da Buhari, Lalong yace an samu cigaba sosai a yanayin tsaron jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya kara da cewa ba da jimawa ba idan komai ya cigaba da tafiya a haka, za'a ɗage dokar hana fita da aka saka a wasu yankuna.

Gwamnan yace:

"Abinda muka tasa a gaba shine mu tabbatar da an gudanar da sahihin bincike kuma an gurfanar da duk wanda ke da hannu, domin ya girbi abinda ya shuka."
"Kun sani cewa sojoji da yan sanda a karakashin shugaban ƙasa suke, amma a halin yanzin suna aiki a jihata ba kama hannun yaro."
"Shiyasa a ranar farko, muka saka dokar hana fita ta awa 24, daga baya muka sassuata wa mutane. Insha Allahu a wannan makon zamu sake sassauta dokar domin baiwa mutane damar cigaba da harkokinsu."

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

Buhari ya ɗauki alkawari

Gwamna Lalong yace shugaba Buhari ya yi alkawarin tallafawa waɗanda lamarin ya shafa na baya-bayannan, waɗan aka raba da muhallansu.

Ya kara da cewa ya roki shugaban da a tallafa wa wafanda aka raba da muhallansu da kayan rage raɗadi, kuma shugaban ya yi alakwarin taimakawa.

A wani labarin kuma Pantami yace ya Samar da Isasshen Fasahar Zamani da Za'a Magance Matsalar Tsaro a Najeriya

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Pantami, yace ya yi bakin kokarinsa wajen samar da isashen fasahar zamani da zai taimaka wa hukumomin tsaro su magance matsalar tsaro a faɗin kasar nan.

Ministan yace duk abinda hukumomin tsaro suka bukata daga ɓangarensa yana samar musu ɗari bisa ɗari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel