Ku daina miyagun kalamai game da tubabbun ƴan Boko Haram, ku yi musu zaton alheri, FG

Ku daina miyagun kalamai game da tubabbun ƴan Boko Haram, ku yi musu zaton alheri, FG

  • Gwamnatin tarayya ta ja kunnen ‘yan Najeriya a kan yada labaran karya da kazafi a kan tubabbun ‘yan Boko Haram
  • Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya yi wannan furucin a wata tattaunawa da aka yi dashi ranar Juma’a
  • Ministan ya musanta batun horar da tubabbun mayakan Boko Haram zuwa sojojin Najeriya don su taya samar da tsaro

Washington - Gwamnatin tarayya ta ja kunnen ‘yan Najeriya a kan yadda suke yawo da labaran karya dangane da tubabbun mayakan Boko Haram.

Vanguard ta ruwaito yadda ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da NAN ta yi dashi a ranar Juma’a a birnin Washington.

Ku daina migayun kalamai game da tubabbun ƴan Boko Haram, ku yi musu zaton alheri, FG
Ku daina migayun kalamai game da tubabbun ƴan Boko Haram, ku yi musu zaton alheri, FG. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

'Yan Boko Haram masu yawa sun yi mubaya'a

An samu rahotanni a kan dubannin ‘yan Boko Haram da iyalansu suka yi mubaya’a ga sojojin Najeriya kuma suka mika wuyansu a Konduga, Bama da Mafa.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Ministan ya nuna takaicinsa kan yadda mutane da dama suke ta musanta cewa asalin mayakan Boko Haram ne suka yi mubaya’ar, sannan idan har da gaske su ne, ya kamata a harbe su don ba su cancanci yafiya ba daga gwamnati da kuma ‘yan Najeriya.

Ya musanta labaran bogin da jama’a suke ta yada wa a kan cewa za a horar da tubabbun mayakan su zama sojojin Najeriya masu yaki da ta’addanci.

Kamar yadda ministan yace, ya kamata a ce ‘yan Najeriya su dinga yaba wa gwamnati da sojoji a kan jajircewarsu kan ganin sun kawo karshen rashin tsaro.

'Yan Najeriya sun dinga cece-kuce kan tubabbun

Idan baku manta ba watanni biyu da suka gabata, ‘yan Najeriya sun yi ta cece-kuce suna bukatar gwamnatin tarayya ta horar da wasu sojojin don a taru a kashe mahaukacin kare.

Kara karanta wannan

Majalisar Dinkin Duniya ta tono sirrin Gwamnatin Tarayya wajen kawo karshen yakin Boko Haram

Sai dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hankalinsa sannan ya yi imani da cewa sojojinmu suna da kokari da kuma dagiyar da za su iya yakar ta’addanci.
Mun gode wa Ubangiji da ya bamu Shugaba Buhari don har da kokarinsa ne yasa ake samun tarin nasarori a kan ganin karshen rashin tsaro.
Kokarinsa ne wurin ganin ya samar wa da sojoji walwala shi ya janyo yanzu haka suke samun kwarin guiwa akan yaki akan ta’addanci,” a cewarsa.

Ya ce batun yafe wa tubabbun ‘yan Boko Haram sunna ce wacce aka gada a duniya, kuma hanya ce ta samar da zaman lafiya a fadin duniya, Vanguard ta ruwaito.

Borno: An kama Malam Ayu da ya amshe miliyoyi hannun wani da sunan zai mayar da shi attajiri cikin sati biyu

A wani labari na daban, jami'an hukumar yaki da rashawa na EFCC a Maiduguri jihar Borno sun kama mutane biyu kan zargin 'asirin samun kudi' a jihar Borno, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa ba zamu iya kashe yan Boko Haram da suka mika wuya ba, Lai Mohammed

A cewar EFCC, daya daga cikin wadanda ake zargin, mai suna Malam Ayu Sugum, ya umurci wani Abubakar Bakura ya sato N2.9m daga wurin wanda ya ke yi wa aiki.

Sugum, da aka gano cewa yana ikirarin cewa yana aiki da iskokai, ya yi wa Bakura alkawarin cewa zai yi masa asiri ta yadda zai zama attajiri cikin kwanaki 14, rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel