Garin Dadi: Kasar turai, inda za ka iya sayen katafaren gida a kasa da N500

Garin Dadi: Kasar turai, inda za ka iya sayen katafaren gida a kasa da N500

  • A kasar Italiya, an samu wani gari da mutum zai iya mallakar gida da kudi kasa da N500
  • Wannan ya faru ne ba wai don garin bai da kyau ba, kawai dai saboda kasancewarsa tsoho
  • Magajin garin ya tabbatar da wannan labari, ya kuma bayyana yadda tsarin siyarwar yake

Legit ta tattaro muku labari mai kamar almara, yayin da bincike ya bankado cewa, akwai wani gari a kasar Italiya, inda mutum zai iya mallakar gida da karamin kudin da bai haura £1 wanda yake kwatankwacin N483.28 na Najeriya.

Yanzu haka a garin mai suna Maenza ana siyar da tsoffin gidaje kuma an ba da rahoton cewa karin iyalai na tururuwan fitowa don sayar da tsoffin gidajensu.

Garin Dadi: Kasar turai, inda za ka iya sayen katafaren gida a kasa da N500
Garin da ake siyar da gidaje araha | Hoto: ecr.co.za
Asali: UGC

Mutane da dama za su ga wannan batu ba komai bane illa zamba, duk da haka, an nakalto magajin garin Claudio Sperduti a kafafen yada labarai daban-daban da ke tabbatar da yarjejeniyar.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

A garin Maenza an saukar da farashin kadarori zuwa £1 (N483.28)

Gidan Rediyon East Cost na dauke da wannan labarin, inda yake ba da rahoton cewa Maenza tana da nisan kilomita 70 a wajen Rome kuma tana cikin yankin Latium.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gidan rediyon ya kuma ce gwamnatin kasa da karamar hukuma ce ta kaddamar da sabon shirin aikin gidaje a bara. Manufarta ta farko ita ce ta taimaka a dawo da kauyuka da garuruwan da har yanzu ke fama da yawan tsufa.

Muna so mu karfafawa mutane

A cewar magajin garin Sperduti, iyalai da dama suna tuntubar hukuma don ba da tsoffin gidajensu kuma sun yi bayanin yadda tsarin yake ta hanyar hira da CNN.

Yace:

“Muna daukar mataki daya bayan daya. Yayin da iyalai na asali suka tuntube kuma suka ba mu tsoffin gidajensu, muna sanya su a kasuwa ta hanyar manna allon sanarwa ga jama'a akan kafar yanar gizon mu don yin komai a bayyane.”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

A lokaci guda kuma, magajin garin ya ce matakin siyar da wadannan gidajen duk manufarsa shi ne hana masu gidajen haya da masu handama daga kwace tsoffin gidajen don samun kudi, kuma wa'adin da aka deba na farko a shirin za a rufe shi ranar Asabar, 28 ga Agusta.

Ya kara da cewa:

"Iyalai da matasa galibi suna barin kauye su kaura zuwa manyan gidaje a biranen da ke kusa da kauyuka, amma ko yaushe akwai sabon shiga wanda ke maye gurbinsu don haka batun ya daidaita tunda har yanzu akwai masu sha'awar tsoffin garuruwa domin su shaki iska mai kyau."

'Yar musulma ta samu tallafin fasto, mahaifiyarta ta durkusa a coci domin nuna godiya

A wani labarin, Shahararriyar malamar addinin kirista Fasto Rose Kelvin, wadda ta kafa cocin Prophetess Rose Kelvin Ministry, ta bai wa wata yarinya Musulma 'yar shekara 12 mai suna Latifat tallafin karatu.

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Da ake ba da labarin yadda lamarin ya kasance, Fasto Rose Kellvin, wacce aka fi sani da Mummy Rose an ce tana neman mai aikin gida ne lokacin da ta hadu da yarinyar.

Lokacin da ta ga matashiyar cewa za ta iya yi mata aikin gida, Rose ta tambayi halin da take ciki kuma ta fahimci cewa Latifat ta bar zuwa makaranta saboda matsalar kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel