Da wanne ido zaku kallemu, kun ji kunya sosai, 'Yan Najeriya sun caccaki hukumomin NDA

Da wanne ido zaku kallemu, kun ji kunya sosai, 'Yan Najeriya sun caccaki hukumomin NDA

  • ‘Yan Najeriya sun bayyana mamakinsu karara a kan yadda ‘yan bindiga suka afka har cikin NDA
  • An samu rahotanni akan yadda ‘yan bindiga suka fada har barikin Afaka ta NDA da safiyar Talata
  • Mutane da dama suna ganin tsabar rashin tsaron kasar nan ne ya janyo hakan, babu wanda zai tsira kenan

Kaduna - ‘Yan Najeriya sun bayyana mamakinsu a kan yadda ‘yan bindiga suka kai farmaki har NDA.

Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka afka har barikin Afaka dake NDA da safiyar talata.

A nan ne suka harbe wani Lieutenant Commander Wulah da wani Lieutenant CM Okoronwo take a nan suka ce ga garinku. Sannan sun yi garkuwa da wani soja.

Da wanne ido zaku kallemu, kun ji kunya sosai, 'Yan Najeriya sun caccaki hukumomin NDA
Da wanne ido zaku kallemu, kun ji kunya sosai, 'Yan Najeriya sun caccaki hukumomin NDA. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wasu mutane suna ganin farmakin yana nuna irin tsabar rashin tsaron dake kasar nan ne, yayin da wasu suke ganin tabbas babu wanda ya tsira a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sunayen hafsoshin soji 2 da 'yan bindiga suka sheke a NDA Kaduna

'Yan Najerya sun yi martani

Wani Musa Auwal ya yi tsokaci da:

Idan har za a kai farmaki NDA, lallai babu wanda ya tsira a kasar nan. Muna bukatar addu’a kwarai a kasar man.

Wani Abd Ler Thev yace:

In dai har ‘yan bindiga za su shiga bariki, rashin tsaron Najeriya ya ta’azzara.
Zan iya bugun kirji in ce sojoji ba za su iya tsare rayuwarmu da dukiyoyin mu ba, kamar yadda suke cika baki.

Sani Salhu Dauda kuwa ya ce:

Kila wannan zai janyo su mike tsaye wurin ganin bayan ‘yan bindiga ko kuma mu fece mu bar kasar nan.

Wani Sharu Babangida yace:

Wannan abin kunya har ina? An fara kai wa wadanda suke da alhakin tsaro farmaki.

Wani kuwa cewa yayi:

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

Gobe zaku gansu da takardu suna neman yafiyar ‘yan Najeriya. Sai gwamnatin APC tace za mu nemi hanyar shiryatar da shedanun mutanen nan sannan su dawo su ci gaba da rayuwa cikin mutane. Gaba daya abin ban takaici gare shi.

'Yan sanda da sojoji sun tsananta sintiri ta kasa da jiragen sama a Zamfara

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Zamfara da wasu jami'ai daga hukumomin tsaro da suka hada da sojoji sun tsananta sintirin sama da kasa a yankin Gusau zuwa titin Tsafe zuwa Yankara dake karamar hukumar Tsafe ta jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wannan na kunshe ne a wata takarda da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau.

Akwai rahotannin sirri da suka bayyana cewa 'yan bindiga na barazanar kai hari wasu yankunan karamar hukumar Tsafe dake jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel