2023: APC na fuskantar sabuwar barazana yayin da Atiku da Obaseki suka hadu kan yadda PDP za ta kada jam'iyyar

2023: APC na fuskantar sabuwar barazana yayin da Atiku da Obaseki suka hadu kan yadda PDP za ta kada jam'iyyar

  • Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce tarurrukan sulhu da ke gudana tsakanin shugabannin PDP na samun sakamako mai kyau
  • Abubakar ya bayyana haka a Benin, babban birnin jihar Edo, a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta, bayan ganawa da gwamna Obaseki
  • A cewarsa, za a karfafa babbar jam'iyyar adawa a kasar don karbe mulki a 2023 daga APC

Benin, Edo - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta ya ayyana cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tana da kyakkyawan matsayi yanzu don kawar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki daga mulki a 2023.

The News ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana hakan a Benin, babban birnin jihar Edo, inda ya kara da cewa ziyarar wani bangare ne na shawarwari kan yadda za a karfafa PDP don karbe mulki daga hannun APC gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Atiku ya tura sako ga PDP, ya ce duk rintsi a kwace mulki a hannun Buhari a 2023

2023: APC na fuskantar sabuwar barazana yayin da Atiku da Obaseki suka hadu kan yadda PDP za ta kada jam'iyyar
Atiku ya ce PDP za ta kwace mulki daga hannun APC a 2023 Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa Atiku ya shaidawa manema labarai bayan ganawar cewa tattaunawarsa da gwamna Obaseki ya ta'allaka ne kan mulki, yanayin da kasar ke ciki da kuma yadda za a karfafa jam'iyyar PDP don karbe madafun iko a shekarar 2023.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Musamman, mun tattauna game da shugabanci, halin da ake ciki a ƙasar, mun tattauna game da jam'iyyarmu, yadda yakamata a ƙarfafa jam'iyyarmu da kuma karɓar jagoranci a jihohi da dama da kuma gwamnatin tarayya."

Obaseki yayi kira da a sake gina PDP kafin zaben shugaban kasa na 2023

Gwamna Obaseki ya kuma ce akwai bukatar sake gina babbar jam’iyyar PDP gabanin zaben shugaban kasa na 2023 domin ceto Najeriya daga matsalolin da take fuskanta.

Obaseki ya ce:

"Dole ne mu baiwa 'yan Najeriya kwarin gwiwa, halin da muke gani a kasashe da dama masu rauni, bayan barkewar cutar ba ta da kyau ko kadan. Dole ne mu tashi a matsayin jam’iyya kuma kada mu jira lokacin zabe, yawancinmu mun fara aikinmu yanzu don ceto Najeriya.

Kara karanta wannan

PDP: Gwamnatin Buhari na amfani da EFCC wajen cin zalin 'yan adawarta na PDP

"Da farko, muna buƙatar gina wata jam’iyya mai ƙarfi don ceto Najeriya, na kasance a gefe guda, a bayyane yake cewa akwai jam'iyya ɗaya a Najeriya, wanda ita ce PDP."

Obaseki ya bayyana abin da ya kira karancin abinci mai zuwa da tsadar kayan abinci a matsayin abin tsoro mafi girma a kasar.

Ya kara da cewa a halin yanzu kasar na cikin mawuyacin hali na tattalin arziki a tarihin kasancewarta kasa.

Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa Obaseki ya jinjinawa Atiku saboda gudunmawar da ya bayar wajen cigaban dimokradiyya.

Ya gode wa Atiku kan kyakkyawan jagoranci, shawarwarin da ya ba shi a lokacin zabensa, ya kara da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya tattauna ta sirri, kuma ya taimaka masa lokacin da shi da magoya bayansa suka bar APC zuwa PDP.

APC: Rigimar Ministan cikin gida da Gwamna ya yi kamari, an sheka da magoya-baya zuwa kotu

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa nake kunyar kasancewa dan APC, tsohon Shugaban majalisar dattawa ya magantu

A wani labarin, an gurfanar da sakataren rikon kwarya na jam’iyyar APC a jihar Osun, Hon Rasaq Salinsile da wasu manyan APC a wani kotun majistare a Osogbo.

The Nation ta rahoto cewa an gurfanar da Rasaq Salinsile, da tsohon shugaban APC, Elder Adelowo Adebiyi da wasu tsofaffin kwamishinoni a kotun.

Wadannan tsofaffin kwamishinoni biyu na jihar Osun sun yi aiki a gwamnatin Rauf Aregbesola, wanda yanzu ba a ga maciji da gwamna Gboyega Oyetola.

Asali: Legit.ng

Online view pixel