APC: Rigimar Ministan cikin gida da Gwamna ya yi kamari, an sheka da magoya-baya zuwa kotu

APC: Rigimar Ministan cikin gida da Gwamna ya yi kamari, an sheka da magoya-baya zuwa kotu

  • An gurfanar da wasu kusoshin APC a kotu, ana zarginsu da ji wa wani rauni
  • Na-kusa da tsohon Gwamna, Rauf Aregbesola ne ake tuhuma da laifi a Osun
  • Magoya bayan Ministan ba su ga maciji da Gwamna mai-ci Gboyega Oyetola

Osun - An gurfanar da sakataren rikon kwarya na jam’iyyar APC a jihar Osun, Hon Rasaq Salinsile da wasu manyan APC a wani kotun majistare a Osogbo.

The Nation ta rahoto cewa an gurfanar da Rasaq Salinsile, da tsohon shugaban APC, Elder Adelowo Adebiyi da wasu tsofaffin kwamishinoni a kotun.

Wadannan tsofaffin kwamishinoni biyu na jihar Osun sun yi aiki a gwamnatin Rauf Aregbesola, wanda yanzu ba a ga maciji da gwamna Gboyega Oyetola.

Wani laifi suka aikata?

Ana zargin Kazeem Salami, Biyi Odunlade da hadiman tsohon gwamna, Gbenga Akano da Alaba Popoola da Azeez Adekunle da laifin gwabje wani mutum.

Kara karanta wannan

Wadanda suka halarci walimar Yusuf Buhari da Zahra Bayero sun samu Iphone 12 Pro, Ipad

Lauyan jami’an ‘yan sanda, John Idoko ya shaida wa kotu cewa wadannan mutane sun hada-kai ne sun rotsa kan Hamzat Lukman Babatunde da duwatsu.

John Idoko yace wannan lamari ya auku ne a ranar 14 ga watan Agusta, 2021, inda aka ji masa rauni. Wadanda ake tuhuma sun musanya wannan zargin.

Ministan cikin gida da Gwamnan Osun
Oyetola da Aregbesola a wurin Buhari Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya shari'ar ta kasance?

Lauyoyin da suke kare wadanda ake zargi da laifi; Muftau Adediran da Abdulfatai Abdulsalam sun bukaci a ba su beli, kuma Alkali ya amince da hakan.

Mai shari’a, Dr. Olusegun Ayilara ya bada belin Salinsile, Adebiyi, Salami, Odunlade da Akano a kan Naira miliyan biyar tare da kawo wanda zai tsaya masu.

Alkali mai shari’a, Dr. Olusegun Ayilara ya daga shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Satumba, 2021.

Rigimar Rauf Aregbesola da Gboyega Oyetola

Kara karanta wannan

An hallaka makiyaya 3 a wani sabon harin ramuwar gayyar 'yan bindiga a Kaduna

Daily Trust tace an dade ana fama da rikicin cikin gida tsakanin mutanen Rauf Aregbesola da na magajinsa, Adegboyega Oyetola, har hakan ya kai ga fada.

Magoya bayan Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, sun ce ba a tafiya da su a gwamnatin Adegboyega Oyetola, yunkurin sulhu ya ci tura.

Takarar Godswill Akpabio

A yau ne aka ji cewa kungiyar'Senator Akpabio for Common Good, ta ce tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya fi dace wa ya zama Shugaban kasa.

Senator Akpabio for Common Gooda ce ba tsoron EFCC ya sa Sanata Akpabio ya bar PDP, ya bi APC ba. Shugaban kungiyar yace ba a taba samun Ministan da laifi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel