Wadanda suka halarci walimar Yusuf Buhari da Zahra Bayero sun samu Iphone 12 Pro da Ipad

Wadanda suka halarci walimar Yusuf Buhari da Zahra Bayero sun samu Iphone 12 Pro da Ipad

  • Rabon Iphone 12 Pro aka yi a wajen walimar Yusuf Buhari da Zahara Bayero
  • An ga sababbin wayar IPhone dauke da sunan Amarya da Ango da aka kyautar
  • Rabon wadannan kaya masu tsada ya jawo mutane suna ta surutu a Facebook

Abuja - Legit.ng Hausa ta samu labari cewa an raba kaya masu tsada a matsayin tukwuici ga wadanda suka samu halartar bikin ‘dan shugaban Najeriya.

Kamar yadda hotuna da bidiyoyi suka nuna an raba wani kwali da yake dauke da wayar Iphone da kuma na’urar Ipad, duk na kamfanin Apple, a wajen bikin.

An yi wa wannan kwali tambari da sunayen amarya da ango da ranar aurensu. A ciki za a ga dambareriyar wayar Iphone 12 Pro wanda ake yayi a Duniya.

Kara karanta wannan

An hallaka makiyaya 3 a wani sabon harin ramuwar gayyar 'yan bindiga a Kaduna

Haka zalika an sa man shafawa, littatafan rubutu da kuma kwalbar lemu a cikin kwalin kayan kyautan.

Bugu da kari a wani kwali na dabam, akwai sabuwar na’urar Ipad ta zamani. A jikin Ipad din da wayar ta IPhone 12 Pro, akwai sunayen amarya da angonta.

Ganin wadannan kaya na musamman da aka ba mahalarta, mutane sun fito suna ta tofa albarkacin bakinsu, musamman a irinsu dandalin Facebook.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me mutane ke fada?

Injiniya Aminu Bello yace da wannan dawainiyar miliyoyi da aka yi, za a iya sayen tireloli a raba wa ‘yan gudun hijiran da jihohin Katsina da Zamfara kayan abinci.

Muhammad T. Shehu kuwa cewa ya yi dangin amarya watau Mai martaba, Nasiru Ado Bayero ne suka dauki nauyin raba wadannan kaya masu ‘dan Karen tsada.

Rabi’u Biyora ya buge ne da da-na-sani, yace da ya san za a samu IPhone 12 Pro da IPad, da ya halarci walimar ko da zai biya kudin jirgi, domin zai tashi da riba.

Kara karanta wannan

Magama-Saminaka: An yi kira ga Gwamnatoci su gyara titin da zai sa a daina kashe Matafiya a Jos

Zahra Nasiru Bayero da Yusuf Buhari
Zahra Nasiru Bayero da Yusuf Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Kamfanin apple ya bada na shi gudunmuwan Shine Baba yace a raba ma talakawa saboda son da yake masu

– Aliyu Tafashiya

Duk kanwan jace! Talaka yakamata kwatakwata yadaina tunanin akwai mai sonshi a Nigeria

– Isa Maina

Kabiru Danladi wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa, ya tuna da yadda aka raba manyan wayoyin IPhone a lokacin da Goodluck Jonathan ya aurar da 'ya 'yansa a 2014.

A karshen makon jiya ‘dan shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari, ya auri sahibarsa gimbiyar Sarkin Bichi, Zahra Nasiru Bayero, aka yi walima a Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel