An kame wani saurayi da ya dirkawa budurwa ciki, ya kashe, ya binne ta a Adamawa

An kame wani saurayi da ya dirkawa budurwa ciki, ya kashe, ya binne ta a Adamawa

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Adamawa sun cafke wasu matasa da laifin kashe wata budurwa
  • Rahoto ya bayyana yadda matasan suka hada kai wajen kashe wata budurwa Franca Elisha
  • Bayan tabbatar da ta mutu, sun kwashi gawarta suka binne a wani dan karamin rami mara zurfi

Adamawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta gurfanar da wani dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Mubi, Mumuni Abubakar, bisa zargin kashe budurwarsa mai juna biyu, Franca Elisha, tare da binne gawarta a cikin rami mara zurfi.

Rundunar ta kuma gurfanar da wasu abokansa biyu, Huzaifa Shuaibu da Rabiu Adamu, saboda rawar da suka taka dumu-dumu a lamarin, Punch ta ruwaito.

Franca Elisha, dalibar Diploma a Sashen Kimiyyar Laburare a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya dake Mubi, an binne ta a cikin rami mara zurfi bayan kokarin zubar da ciki da ta yi ya faskara.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

An kame wani saurayi da ya dirkawa budurwa ciki, ya kashe, ya binne ta a Adamawa
Motar rundunar 'yan sanda | Hoto: irinnews.org
Asali: UGC

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, ya ce korafin da iyayen marigayiyar suka yi game da inda take ya kai ga binciken da ya gano yanayin da ke tattare da mutuwar ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mumuni Abubakar, mazaunin Unguwar Sanda dake karamar hukumar Yola ta Arewa, ana zargin ya dirkawa Franca ciki, kuma da ta sanar da shi, sai ya dage cewa lallai ne ta cire cikin.

Rahoton Farko na ‘yan sanda ya ce:

“Ya kai marigayiyar dakinsa da ke unguwar dalibai a bayan jami’ar jihar don zubar da cikin a asirce a ranar 6 ga Agusta, 2021.
“Don samun nasarar aiwatar da shirin zubar da cikin, wanda ake tuhuma ya gayyaci abokinsa kuma dalibin Kwalejin Kiwon Lafiya da Fasaha dake Mubi, Huzaifa Shuaibu, wanda ya yi amfani da miyagun kwayoyi da allurai don cire dan a cikin mahaifar Franca.”

Kara karanta wannan

Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa

An yi zargin allurar ta jawo wa Franca wani nau'in tashin hankali, yayin da ta mutu.

Mumuni, a cikin bayanin furucinsa, ya ce budurwar tasa daga baya ta farfado.

A cewarsa:

"Amma don cimma zubat da cikin, Shuaibu ya sake tsikara mata allurar bayan ta farfado.
“Abin takaici, ta suma a karo na biyu kuma ba ta farfado ba; daga baya ta mutu.”

Wadanda ake zargin sun gayyaci Adamu, wani abokinsu, domin ya taimaka wajen kawar da gawar Franca.

Abubakar ya ce:

"Mun dauki gawar muka binne a cikin rami mara zurfi tare da wayar hannu da katin shaidar zama dan kasa, sannan muka ci gaba da rayuwarmu ta yau da kullum, muna yin kamar ba abin da ya faru."

Wata budurwa ta bakunci lahira yayin da take lalata da saurayinta a mota

Mutuwa ta dauke wata budurwa mai suna Gabrielly Dickson a yayin da suke tsaka da fasikanci da saurayinta mai shekaru 26 a cikin mota.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

An garzaya da budurwar mai shekara 15 zuwa asibiti ne bayan saurayin nata da yake fasikanci da ita ya lura cewa ta fita daga hayyacinta, in ji Aminiya.

’Yan sanda da ke binciken lamarin sun ce saurayin, wanda ake kira “babban mai taimako”, ya shaida musu cewa yana cikin saduwa da ita a cikin mota ne ya lura labbanta da fatar jikinta sun koma fari fat, hannuwanta kuma sun jujjuye.

Ko da aka kai ta asibiti, likitoci sun gano zuciyarta ta buga, amma babu yadda suka iya, washegari da safe kuma ta sheka lahira.

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

A wani labarin, Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) tare da hadin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro sun cafke wata budurwa yar shekara 22 mai suna Gloria Okolie.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwar da mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Aremu Adeniran, ya fitar kuma Legit.ng Hausa ta samu a ranar Lahadi, 22 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Adeniran ya lura cewa an kama Okolie ne saboda hada kai da ta yi a cikin jerin hare-haren da aka kai da gangan kan jami'an tsaro, wasu muhimman wurarenmallakin kasa ciki har da ofisoshin INEC da kashe jami'an tsaro a yankin kudu maso gabashin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel