An cimma nasara: Minista Pantami ya ce saura kiris 5G ya fara aiki a Najeriya

An cimma nasara: Minista Pantami ya ce saura kiris 5G ya fara aiki a Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya ta shirya tsaf domin fara dasa cibiyar sadarwar 5G a cikin Najeriya
  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami ne ya bayyana hakan ga NAN
  • Wannan na zuwa ne bayan gudanar da cikakken bincike ta fuskoki da yawa in ji Dr Pantami

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta dasa cibiyar sadarwa ta 5G a cikin kasar don kara gudun cudanyar yanar gizo, in ji TheCable.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani Isa Pantami ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

Pantami ya ce shawarar dasa cibiyar sadarwa ta 5G ta biyo bayan sakamakon cikakken bincike, kwakwaf da gwajin kawar shakku kan barazana ga tsaro ko kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Ya yi bayanin cewa aiki kan manufofin kasa na 5G ya kai 95% kuma za a gabatar da shi ga majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a kan kari.

Bayan cimma babbar nasara, minista Pantami ya ce saura kiris 5G ta fara aiki a Najeriya
Tsarin sadarwa na 5G mai gudun gaske | Hoto: quinkpost.com
Asali: UGC

Pantami, wanda ya ce babban abin da ya fi damun gwamnati shi ne tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan Najeriya wajen amfani da ayyukansu a bangaren sadarwa, ya dora laifin jinkirin da aka samu na dasa cibiyar sadarwa ta 5G kan wasu makiran shakku da ake yadawa.

A cewarsa:

“Gwamnatin mu mai sauraran mutane ce; don haka muna sauraron sukar da ta dace, muna girmama hakan kuma muna yabawa kuma akalla muna kimanta aikatawa.
"Mun kai kololuwar mataki kan 5G, to, wani batun ya taso cewa 5G yana da alaka da Korona; mutane da yawa ciki har da masu ilimi sun fara yayata batun ba tare da tantancewa ba.

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

“A zahiri, mutane sun dan tsorata kuma suna shakkar fasahar.
"Don haka mun ba da isasshen lokaci don yin karin shawarwari, kirkirar shirin wayar da kan jama'a a cikin yarukan gida don wayar da 'yan kasar mu saboda magance duk wani kalubale.
“Mun kafa wata tawaga ta fasaha wacce ta dace da tsaro, kiwon lafiya da cibiyoyin muhalli da kuma ma’aikatan gwamnati domin mu kasance a bangare daya.
"Ina so in ba ku tabbacin cewa cibiyar sadarwar 5G tana cikin tsarin sanarwa mai kyau."

An fara batun kasuwancin 5G da hukumar NCC

Pantami ya ce ma’aikatar sadarwa ta fara tattaunawa da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) game da kasuwancin cibiyar sadarwar 5G, Punch ta tattaro.

“Daga wannan gaba, NCC za ta ba masu gudanar da ayyukan wayoyin hannu don fara dasawa; don haka, aikin kusan a shirye yake.
"Na je Majalisar kasa, na kare gabatarwar mu kuma sun yarda, sun kuma amince da dasa 5G.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

"Sun kuma karfafa mana da mu yi koyi da wasu kasashe wadanda suka dasa 5G kuma mun riga mun yi hakan.
"Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar da sanarwa cewa babu wata alaka tsakanin cibiyar sadarwar 5G da Korona kuma hakan na magance matsalar lafiya.
"Hakanan, Kungiyar Sadarwa ta Duniya (ICU), wacce reshen Majalisar Dinkin Duniya ce, ita ma ta fitar da wata sanarwa da ke karyata duk wani tasirin sharri daga 5G."

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur

A wani labarin, Rahoton da muke samu daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur.

Legit.ng Hausa ta samo wata sanarwar mai ba shugaba shawari na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, inda ta bayyana rattaba hannun shugaban a yau Litinin 16 ga watan Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Femi Adesina ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur na shekarar 2021 don zama doka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel