Da duminsa: EFCC ta sako tsohon gwamna bayan damke shi da tayi da sa'o'i

Da duminsa: EFCC ta sako tsohon gwamna bayan damke shi da tayi da sa'o'i

  • EFCC ta sako tsohon gwamnan jihar Abia kuma sanata mai wakilyar Abia ta tsakiya, Sanata Orji
  • Dama a ranar Alhamis 19 ga watan Augusta hukumar ta kama shi a filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja
  • Hukumar ta bayyana cewa an baiwa sanatan umarnin bayyana a ofishinta a ranar Juma’a, 20 ga watan Augusta don amsa wasu tambayoyi

FCT, Abuja - An sako tsohon gwmanan jihar Abia, Sanata Theodore Orji bayan kwashe wasu sa’o’i a ofishin EFCC.

Gidan talabijin din Channels sun ruwaito yadda jami’an hukumar EFCC sun damki sanatan a filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja a ranar Alhamis, 19 ga watan Augusta.

Da duminsa: EFCC ta sako tsohon gwamna bayan damke shi da tayi da sa'o'i
Da duminsa: EFCC ta sako tsohon gwamna bayan damke shi da tayi da sa'o'i. Hoto daga T. A. Orji
Asali: Facebook

Hukumar EFCC ta sako tsohon gwamnan bayan ya sha tambayoyi a kan harkokin kudaden da yayi tsakanin 2007 da 2015 inda ake zargin rashawa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hukumar EFCC Ta Cafke Tsohon Gwamna da Ta Jima Tana Nema a Filin Jirgi

EFCC ta ce shekarar da ta gabata Sanata Orji ya bayyana gabanta yana bukatar su sakar masa wasu takardu da za su bashi damar fita Dubai don duba lafiyarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar ta kula da yadda sanatan ya ki mayar da takardun bayan ya dawo daga tafiyar tasa.

Don haka hukumar ta bukaci Orji ya dawo hedkwatarta a ranar Juma’a don ya cigaba da amsa tambayoyi.

Sai dai sanatan ya musanta rike shi da aka yi. A cewarsa jami’an EFCC tsare shi kawai suka yi a hanyarsa ta zuwa London don duba lafiyarsa.

Premium times ta ruwaito yadda gwamnan ya sha tambayoyi tare da dansa Chinedu, kakakin majalisar jihar Abia wanda ya bayyana a ofishin bayan ya ji EFCC ta kama mahaifinsa.

Kokwanto kan tubabbun Boko Haram: Akwai lauje cikin nadi ko tuban mazuru ne?

Kara karanta wannan

Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa

Jama’a da dama sun yi ta kokwanto akan tubabbun mayakan Boko Haram har wasu suna cewa da kyar idan da gaske su din ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu kuma sun fi yarda da cewa wasunsu da suka dauki makamai suna yakar anguwanni da jama’an jiha sun mika wuya ne kawai don karfinsu ya kare kuma basu da wata mafita da ta wuce su shiga sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta bude na yafiya don su mori tagomashi.

Sai dai a ranar Laraba aka tuntubi darektan yada labaran soji, Manjo janar Olufemi Sawyer inda ya musanta duk wadannan maganganun yace ya kamata ‘yan Najeriya su rage yada jita-jita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel