Hotuna da bidiyoyin liyafar cin abincin dare na auren Yusuf da Zahra, Ali Jita da Breaker sun bajekoli

Hotuna da bidiyoyin liyafar cin abincin dare na auren Yusuf da Zahra, Ali Jita da Breaker sun bajekoli

  • Jinin sarauta ne suka hadu da masu mulki a yayin da aka yi liyafar cin abincin dare ta auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero
  • Cike da shigar alfarma da kamala aka ga ango, amarya tare da 'yan uwansu a shagalin da aka yi na ranar Alhamis
  • Mawakan zamani, kuma masu tashe, Ali Jita da Hamisu Breaker Dorayi ne suka nishadantar da wurin da sautikansu

Kano - Haduwar mulki da sarauta ta matukar kayatar da jama'an da suka halarta da wadanda a hoto suka ga liyafar cin abincin dare na bikin Yusuf Muhammadu Buhari, da namiji daya tilo ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da diyar basarake mai izza, mai martaba, Alhaji Nasir Ado Bayero.

A ranar Alhamis, 19 ga watan Augusta, wanda yayi daidai da jajiberin daurin auren masoyan biyu ne aka yi kasaitacciyar liyafar cin abincin dare ta bikin 'yan gatan, kamar yadda shafin @thebeginningofyz suka kawo mana.

Kara karanta wannan

Kayatattun Hotuna da Bidiyoyin Shagalin Kamun Gimbiya Zahra Bayero da Yusuf Buhari

Hotuna da bidiyoyin liyafar cin abinci dare na auren Yusuf da Zahra, Ali Jita da Breaker sun bajekoli
Hotuna da bidiyoyin liyafar cin abinci dare na auren Yusuf da Zahra, Ali Jita da Breaker sun bajekoli. Hoto daga @thebeginningofyz
Asali: Instagram

Babu shakka amarya Zahra da angonta Yusuf sun matukar yin kyau inda aka ga sun yi shiga ta alfarma cikin wasu kaya masu launin sararin samaniya.

'Yan uwan amarya sun dauka shigar alfarma cike da kamala a cikin wani yadi mai launin shudi, launin da ya matukar fito da kyawun fatarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a nan kadai jinin Ado Bayero suka kayatar ba, sun shigo wurin tare da fadawa wadanda ke rike da wata laimar sarauta wacce aka rikewa gimbiya Zahra Nasir Bayero.

'Yan uwan ango sun bayyana a wurin liyafar cike da tasu kalar shigar inda suka shigo tare da wasu masu tsaron lafiyarsu. Babu shakka tsabar mulki ne ke bayyane a tattare dasu.

Daga cikin mawakan da suka nishadantar da wurin da irin sautinsu da baiwarsu, akwai fitaccen mawaki Ali Jita tare da mawaki mai tashe, Hamisu Breaker Dorayi, wanda ya gwangwaje taron da wakarsa ta Jaruma.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyoyin shagalin saka lallen auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero

Kokwanto kan tubabbun Boko Haram: Akwai lauje cikin nadi ko tuban mazuru ne?

Jama’a da dama sun yi ta kokwanto akan tubabbun mayakan Boko Haram har wasu suna cewa da kyar idan da gaske su din ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu kuma sun fi yarda da cewa wasunsu da suka dauki makamai suna yakar anguwanni da jama’an jiha sun mika wuya ne kawai don karfinsu ya kare kuma basu da wata mafita da ta wuce su shiga sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta bude na yafiya don su mori tagomashi.

Sai dai a ranar Laraba aka tuntubi darektan yada labaran soji, Manjo janar Olufemi Sawyer inda ya musanta duk wadannan maganganun yace ya kamata ‘yan Najeriya su rage yada jita-jita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel