Kuma dai: An kashe dalibin jami’ar Jos ‘yan awanni bayan Lalong ya saukaka dokar kulle

Kuma dai: An kashe dalibin jami’ar Jos ‘yan awanni bayan Lalong ya saukaka dokar kulle

  • Wasu da ake zaton 'yan daba sun halaka wani dalibin jami'ar Jos ta hanyar caka masa wuka
  • An tattaro cewa dalibin na a cikin a daidaita sahu lokacin da maharan suka far masa
  • Shuaban kungiyar dalibai ta jami’ar (SUG), Kwamared Danladi Joshua Adankala, ya tabbatar da lamarin tare da yin Alla-wadai da shi

Rahotanni sun kawo cewa wasu ‘yan daba sun caka wa wani dalibin jami’ar Jos wuka har lahira a kusa da makarantar.

Lamarin ya faru ne ‘yan awanni bayan da gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong ya sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Jos ta Arewa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kuma dai: An kashe dalibin jami’ar Jos ‘yan awanni bayan Lalong ya saukaka dokar kulle
Wasu sun halaka dalibin jami’ar Jos ta hanyar caka masa wuka Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na rana lokacin da harkoki ke komawa daidai a hankali a babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa

Shuaban kungiyar dalibai ta jami’ar (SUG), Kwamared Danladi Joshua Adankala, ya tabbatar da ci gaban ga manema labarai a Jos.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, an ciro wanda aka kashe daga adaidaita sahu sannan aka caka masa wuka har lahira.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma wanda bai dace ba.

Ya ce:

“Dalibin ya hau keken adaidaita sahu daga makarantar zuwa babban harabar jami’ar kuma kwatsam a kan hanya, sai aka ciro shi aka caka masa wuka har lahira.
"Hawayenmu na neman adalci ba su haifar da komai ba illa ƙarin radadi, zafi, tsoro, baƙin ciki da kuka mara iyaka.
“Cikin gaggawa, ya kamata gwamnatin jihar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sauƙaƙe gina shingen kewaye na makarantarmu. Yakamata a sami ƙarin dakunan kwanan dalibai. Wannan zai taimaka matuka wajen rage yawan daliban da ke zama a cikin gari.”

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

Gwamna Lalong ya sassauta dokar hana fita a Jos

A baya mun kawo cewa Gwamna Simon Lalong na Jihar Plateau ya sassauta dokar hana zirga-zirga na awa 24 da aka saka a karamar hukumar Jos ta Arewa, bayan kisar matafiya a kan hanyar Rukuba, a wajen garin Jos a ranar Asabar da ta gabata.

A karkashin sabon tsarin, dokar takaita zirga-zirgan za ta fara aiki ne daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe daga ranar Alhamis, 19 ga watan Agustan 2021.

Wannan dokar ta shafi kananan hukumomin Bassa da Jos ta Kudu har zuwa wani lokaci a nan gaba a cewar sanarwar kamar yadda The Herald ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel