Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Lalong ya sassauta dokar hana fita a Jos

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Lalong ya sassauta dokar hana fita a Jos

  • Gwamnan Jihar Plateau, Simon Lalong ya sassauta dokar hana fita na awa 24 da ya sa a wasu yankunan jihar
  • A halin yanzu, sassaucin da aka yi dokar za ta rika aiki ne daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe daga ranar Alhamis
  • Gwamna Lalong ya gargadi mutane cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin mayar da dokar na awa 24 idan wani rikici ya barke

Jos, Jihar Plateau - Gwamna Simon Lalong na Jihar Plateau ya sassauta dokar hana zirga-zirga na awa 24 da aka saka a karamar hukumar Jos ta Arewa, bayan kisar matafiya a kan hanyar Rukuba, a wajen garin Jos a ranar Asabar da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman FEC na farko, ya amince a sayo karnukan N650m

A karkashin sabon tsarin, dokar takaita zirga-zirgan za ta fara aiki ne daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe daga ranar Alhamis, 19 ga watan Agustan 2021.

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Lalong ya sassauta dokar hana zirga-zirga a Jos
Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan dokar ta shafi kananan hukumomin Bassa da Jos ta Kudu har zuwa wani lokaci a nan gaba a cewar sanarwar kamar yadda The Herald ta ruwaito.

An dauki wannan matakin ne bayan taron majalisar tsaro na jihar da aka gudanar a gidan gwamnati a ranar Laraba inda shugabannin hukumomin tsaro suka yi wa gwamnan bayani game da halin da ake ciki a jihar.

Lalonga ya gargadi masu son tada rikici

Gwamna Lalong ya kuma gargadi masu son tada zaune tsaye su shiga taitayinsu ko kuma su gamu da fushin hukuma, wanda tuni an basu umurnin kada su sasauta wa duk wani mai son tada rikici.

Kara karanta wannan

2023: Cancanta ya kamata a bi wajen zabar wanda zai zama Shugaban Najeriya, in ji Yahaya Bello

Ya bayyana fushinsa game da wasu da ya kira a matsayin bata gari da ke tada fitina a jihar bayan an kai wasu hare-hare a jihar da suka yi sanadin rasa rayyuka da dukiyoyi a Jos ta Arewa da Bassa yayin da aka saka dokar ta hana zirga-zirga.

Jami'a tsaro za su cigaba da saka ido kan yanayin tsaro

Yayin da aka sassauta dokar hana zirga-zirgan a Jos ta Arewa, jami'an tsaro za su kafa shinge a yankunan da ake zargin rikici ka iya barkewa kana za a tura jami'an tsaro masu farin kaya domin saka ido kan yadda mutane ke gudanar da harkoki.

Gwamnan ya sake jadadda cewa dokar hana taruwar mutane ko tattaki tana nan har yanzu don haka duk wanda aka samu yana saba dokar za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Ya kuma bukaci iyaye da shugabannin mutane su shawarci na kasa da su domin su zauna lafiya, yana mai cewa gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin sake saka dokar hana zirga-zirgan wanda zai shafi tattalin arziki da walwalar mutanen jihar.

Kara karanta wannan

Ba za mu yarda a sake samun rikicin addini a Filato ba, in ji Lalong

Ba za mu yarda a sake samun rikicin addini a Filato ba, in ji Lalong

A baya mun kawo muku rahoton cewa Gwamna Simon Lalong ya bayyana cewa gwamnatinsa da hukumomin tsaro za su yi duk mai yiwuwa don dakile rikicin addini a jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Gwamnan ya yi magana ne a ranar Litinin lokacin da ya zagaya sassan Jos ta Arewa don sa ido kan bin dokar hana fita na sa’o’i 24.

Lalong ya sha alwashin cewa za a hukunta duk wadanda ke da hannu a rikicin na baya -bayan nan sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel