Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta Saka Ranar Gangamin Tarukanta Na Kananan Hukumomi

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta Saka Ranar Gangamin Tarukanta Na Kananan Hukumomi

  • Jam'iyyar APC ta saka ranar Asabar 4 ga watan Satumba a matsayin ranar da zata gudanar da zaɓukan kananan hukumomi
  • Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da APC ta fitar ranar Laraba a Abuja ɗauke da sa hannun sakarenta
  • A kwanakin bayane APC ta gudanar da zabukan shugabanninta a matakin gunduma

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta sanya ranar 4 ga watan Satumba domin gudanar da gangamin tarukanta na jihohi, kamar yadda punch ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ta fitar a Abuja, mai taken, "APC ta saka ranar Asabar 4 ga watan Satumba domin gudanar da taron kananan hukumomi; ta fara siyar da fom."

Sanarwar na ɗauke da sanya hannun sakataren kwamitin rikon kwarya na APC ta kasa, Sanata John Akpanudoedehe.

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

APC ta saka 4 ga Satumba ranar tarukanta na kananan hukumomi
Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Gangamin Taronta Na kananan hukumomi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewar sanarwar, jam'iyya na cigaba da siyar da fom a halin yanzu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yaushe APC zata gudanar da gangaminta na jihohi?

Legit.ng Hausa ta ruwaito muku cewa jam'iyyar APC zata gudanar tarukan jihohi bayan kammala na kananan hukumomi.

A ranar 31 ga watan Yuli, APC ta gudanar da tarurrukanta na gundumomi, wanda rahotanni suka tabbatar cewa rikici da rashin bin ka'ida ya baibayeshi.

Tun bayan rushe shugabancin jam'iyyar APC ta ƙasa ƙarkashin jagorancin, Adams Oshiomhole, a watan Yuni, 2020, aka kafa kwamitin rikon kwarya bisa kagorancin Mai Mala Buni, wanda ke kula da al'amuran jam'iyyar.

A wani labarin kuma Hujjojin da Aka Kawo Sun Mun Tsauri, Alkalin Kotu Ya Dage Sauraron Karar Sheikh Abduljabbar

Alkalin dake jagorantar shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara da gwamnatin Kano, Ibrahim Sarki Yola, ya ɗage sauraron karar zuwa 2 ga watan Satunba.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Yola ya bayyana cewa hujjojin da lauyoyi suka gabatar a gabansa a zaman kotu na ranar Laraba suna da sarkakiya kuma suna bukatar dogon nazari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel