2023: Cancanta ya kamata a bi wajen zabar wanda zai zama Shugaban Najeriya, in ji Yahaya Bello

2023: Cancanta ya kamata a bi wajen zabar wanda zai zama Shugaban Najeriya, in ji Yahaya Bello

  • Gwamna Yahaya Bello ya ci gaba da kamfen dinsa na adawa da mulkin karba-karba gabanin zaben 2023
  • Gwamnan na Kogi wanda tun da farko ya nuna sha’awar tsayawa takara ya ce cancanta ya kamata a fi ba mahimmancin wajen hawa kujerar
  • Gwamnan ya nanata matsayinsa a wani taron da kungiyar Matasan Najeriya ta gudanar a Lafia

Lafia - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce cancanta ne ya kamata ya zama babban abin da 'yan Najeriya za su fi mayar da hankali a kai, domin su ne za su zabi shugaban kasar na gaba a 2023, jaridar Punch ta ruwaito.

Bello ya fadi hakan ne a jawabin da babban hadiminsa, Mohammed Abdulkareem ya yi a madadinsa a yayin wani taro a jihar Nasarawa a ranar Talata, 17 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

2023: Cancanta ya kamata a bi wajen zabar wanda zai zama Shugaban Najeriya, in ji Yahaya Bello
Yahaya Bello ya ce cancanta ya kamata a bi wajen zabar wanda zai zama Shugaban Najeriya Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook
"Ya zama dole zaɓin wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba a 2023 ya dogara kan wanda ya dace ba wai a kan yankin da ya fito ba."

A halin da ake ciki, jaridar Premium Times ta rahoto cewa Nigerian Indigenous Nationalities Alliance for Self-Determination ta ce babu wani zabe da za a yi a Najeriya a shekarar 2023 sai dai idan gwamnatin tarayya ta amince ta gudanar da kuri'ar raba gardama ga dukkan kungiyoyin da ke cin gashin kansu a kasar.

Shugaban kungiyar, Banji Akintoye, ya ce idan aka dakatar da zaben 2023 a shekarar 2021, Kundin Tsarin Mulkin 1999 zai ba da damar gudanar da zaben raba gardama na yanki don cin gashin kai.

Ya kara da cewa ya kamata a dauki matakin dakatar da shirye -shiryen zuwa babban zaben 2023 cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Kwarewa ya kamata a duba wajen tantance wanda zai gaji Buhari, in ji Yahaya Bello

A wani labarin, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tana shirye-shiryen gaske don samun nasara yayin zaben gwamnan Anambra mai zuwa.

Daya daga cikin irin wannan shirye-shiryen shine kaddamar da kwamitin yakin neman zabe wanda ya kunshi galibin shugabannin jihohi kamar Gwamna Hope Uzodinma, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da Gwamna Yahaya Bello.

Asali: Legit.ng

Online view pixel