APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

  • Ba dukka manyan jiga-jigan APC ne suka yi imanin cewa jam’iyya mai mulki ta yi abin kirki ba tun lokacin da ta hau kan mulki
  • Daya daga cikin waɗanda suka ba jam’iyyar maki mafi karanci a bangarori da dama shine Cif Tony Okocha daga jihar Ribas
  • Jiga-jigan APC a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, sun yi ikirarin cewa a cikin shekaru shida, APC ba ta kawo canji mai kyau ba a Najeriya

Gabanin babban zaben shekarar 2023, wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Ribas, Cif Tony Okocha, ya yi wasu hasashe marasa kyau ga jam'iyyar mai mulki.

A ganin Okocha, lashe zaben shugaban kasa mai zuwa zai kasance babban aiki ga APC saboda 'yan Najeriya sun rasa karfin gwiwa kan ta.

Kara karanta wannan

2023: Yemi Osinbajo ya bayyana abin da zai faru da APC bayan Shugaba Buhari ya bar mulki

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023
Jigon APC ya ce zai yi wahala jam'iyyar ta kai labari a 2023 Hoto: All Progressives Congres
Asali: Twitter

Jigon, wanda yayi magana da Leadership a ranar Talata, 17 ga Agusta, ya lura cewa jam'iyyar da ta hau mulki tare da alƙawarin canza mummunan halin da ake zargin mulkin shekaru 16 na jam'iyyar PDP ya kawo ba ta samu wani ci gaba mai ma'ana ba ta fuskar tattalin arziki, kayayyakin more rayuwa, isar da lafiya, da samar da ayyukan yi.

Ya bayar da hujjar cewa a cikin shekaru shida da suka gabata, babu wani gagarumin ci gaba da aka samu a yanayin rayuwar ‘yan kasa a karkashin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalamansa:

"Idan na waiwaya baya, shekaru shida sun shude, ba zan iya daukar wani abu da mutum zai iya rikewa ya ce eh, wannan shine canjin da muka yi alkawarin kawowa ba. Talauci yana ko'ina.

Kara karanta wannan

Sanusi II: Najeriya ba ta cimma komai ba cikin shekaru 40, dole na fadi gaskiya

"Da kyar 'yan Najeriya ke iya cin abinci, hanyoyi sun yi muni, babu asibitoci har yanzu. A gaskiya mun yi alkawarin cewa kasarmu za ta zama cibiyar yawon bude ido ta neman lafiya, amma har yanzu shugabanmu yana tafiya kasashen waje idan ba shi da lafiya."

2023: Fitaccen jigon APC ya bayyana yankin da zai samar da wanda zai gaji Buhari

A wani labarin, Kashim Ibrahim-Imam, jigo a jam'iyyar ya rufe hasashen fitowar dan takarar shugaban kasa na APC daga shiyyar kudu maso kudu da kudu maso gabas.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa dan takarar gwamnan na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sau biyu, wanda a yanzu jigo ne na APC, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, a wani shiri na Arise TV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel