Zamu kashesu cikin awa 24 idan ba'a biyamu ba, Yan bindigan da suka sace dalibai a Zamfara sun saki bidiyo

Zamu kashesu cikin awa 24 idan ba'a biyamu ba, Yan bindigan da suka sace dalibai a Zamfara sun saki bidiyo

  • Yan bindiga na cigaba da cin karansu ba babbaka a Arewa maso yammacin Najeriya
  • Sun saki sabon bidiyon daliban da suka sace a kwalejin aikin noma dake Zamfara
  • Sun bukaci kudin fansar N350m kafin su saki daliban

Zamfara - Yan bindigan da suka yi awon gaba da dalibai da malamai a kwalejin aikin noma da kimiyar dabbobi, Bakura, sun saki bidiyon daliban dake hannunsu.

A cikin faifan bidiyon mai tsahon dakikai 30, daliban na kira ga gwamna Bello Matawalle ya taimaka ya biya kudin fansa, rahoton PremiumTimes.

A cikin bidiyon, an ga dalibai da ma'ikaata mata tsugunne a kasa idanuwansu a rufe kuma zagaye da yan bindigan masu rike da bindiga kirar AK47.

Daya daga cikin daliban mai rike da wayar yake cewa yan bindigan sun yi alkawarin kashesu cikin sa'o'i 24 idan har ba'a biya kudin fansa ba.

Kara karanta wannan

Muna kashe N8m kulli yaumin wajen ciyar da dalibai a jihar Enugu, Minista Sadiya

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jama'a kun ga halin da muke ciki, mune daliban kwalejin gona dake nan Bakura LGA da aka dauka. A halin yanzu ma muna fuskantar barazana ta kisa daga garesu muddin gwamnati bata dauki mataki na cikin awa 24."
"Wallahi sun kai mu ga gawawwakin daliban Yarkofoji da suka kashe."

Yayinda dalibin ke magana daya daga cikin yan bindiga na cewa:

"Kowa ya gani, ba karya bane gasu nan, kowa ya gani."

Yan bindiga sun kai hari garin Yarkofoji, dake karamar hukumar Bakura ranar Lahadi, bayan awon gaba da sukayi da daliban kwalejin noma.

Mutum takwas suka kashe a Yarkofoji yayinda suka sace mutum 17.

Yan bindiga sun saki bidiyon daliban makarantar Zamfara da suka sace
Yan bindiga sun saki bidiyon daliban makarantar Zamfara da suka sace Hoto: CAAS
Asali: UGC

Wani mazaunin garin, AbdulNasir Abubakar yace daga cikin wadanda aka kashe akwai, Bashiru Dan Alhazai, Atiku Sule Dan-Iya, Isiya kulele, Aliyu Badamasi, Baki Biyu, Kabiru, dss.

Kara karanta wannan

Mun kashe kimanin bilyan 2 wajen ciyar da daliban firamare a jihar Ondo

Wani tsohon ma'aikacin kwalejin wanda yanzu ke aiki da jami'ar jihar Zamfara dake Talata Mafara ya tabbatar da cewa yan bindigan sun turawa wasu iyayen daliban bidiyoyi.

Yace:

"Hakane, ina mai tabbatar muku sun fara tattauna kudin fansa da iyayen."

Kalli bidiyon:

Sun Nemi a Tattara Musu Miliyan N350m

Yan bindigan sun nemi a basu miliyan N350m kuɗin fansa kafin su sake daliban.

Da yake magana da Punch ta wayar salula, shugaban kwalejin, Alhaji Habibu Mainasara, yace barayin sun tuntuɓe shi ta wayar salula.

Yace yan bindiga sun nemi a ba su miliyan N350m kuɗin fansar mutum 20 dake hannun su a yanzun sannan su sako su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel