Taliban: Ba ma gaba da kowa, mun yafe wa duk wadanda suka yake mu a baya

Taliban: Ba ma gaba da kowa, mun yafe wa duk wadanda suka yake mu a baya

  • Kungiyar Taliban ta bayyana afuwarta ga dukkan wadanda suka yake ta a shekarun baya
  • Ta ce, ba ta son gaba da kowa a yanzu, kuma ba yake-yake ne ta sanya a gabanta a yanzu
  • Ta kuma cewa, burinta shi ne samar da zaman lafiya ga kasar, kuma tana shirin cimma hakan

Afghanistan - Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar kowanne dan kasar Afghanistan ya samu damar walwala tana mai cewa ba ta bukatar abokan gaba.

A taron manema labarai da ta gudanar, mai magana da yawun kungiyar Zabihullah Mujahid, wanda ya bayyana a gaban 'yan jarida a karon farko tun bayan da suka kwace iko, ya ce sun 'yantar da kasar.

Taliban: Ba ma gaba da kowa, mun yafe wa duk wadanda suka yake mu a baya
Taliban Forces | Hoto: guardian.co.uk
Asali: Getty Images

A cewarsa in ji rahoton BBC:

Kara karanta wannan

Afghanistan: Sabanin abinda ake tsoro, Taliban za ta dama da mata a mulkinta

"Bayan shekaru 20 na fafutuka kuma mun kori 'yan kasashen waje".
"Wannan lokaci ne na alfahari."
"Muna son tabbatar da ganin Afghanistan ba ta sake tsunduma cikin yaki ba. Mun yafe wa dukkan mutanen da suka yake mu. Gaba ta zo karshe."

Meye Taliban ta sa a gaba?

A rahoton Sky News, Zabihullah ya kara da cewa babban abin da Taliban ta sa a gaba shi ne samar da "doka da oda" ga babban birnin Kabul - kuma ya tabbatar wa mutanen birnin cewa za su "zauna lafiya".

Hakanan ya ba da tabbaci kan amincin wadanda suka yi aiki tare da sojojin Amurka da na kawance.

Ya ce 'yan Taliban "ba sa son su bar kasar" amma yana son su yi amfani da kwarewar su don yiwa sabuwar gwamnatin aiki - kuma "za a yi musu afuwa".

Kara karanta wannan

Bayan hallaka musulmai sama da 20 a Jos, gwamnati ta sanya dokar hana fita

Taliban "ba sa son wasu abokan gaba na ciki ko na waje", in ji shi, sannan kuma ya ce "za mu yi aiki tare da" duniya don kirkirar hanyoyin nasara ga Afghanistan.

Afghanistan: Sabanin abinda ake tsoro, Taliban za ta dama da mata a mulkinta

A wani labarin, Kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan ta sanar da yin afuwa a fadin kasar tare da kira ga mata da su shigo cikin sabuwar gwamnatinta, Aminiya ta ruwaito.

Taliban ta yi hakan ne a kokarinta na kwantar da hankula a Kabul, babban birnin kasar, inda mutane suka yi ta turmitsutsi a filin jirgin sama domin ficewa daga kasar bayan kungiyar ta hambarar da gwamnatin kasar da Amurka ke marawa baya.

Cikin wata sanarwar dauke hannun Enullah Samangani daga hukumar raya al'adu ta Taliban, wacce ita ce ta farko da Taliban ta fitar tun bayan hambarar mulkin shugaba Ashraf Ghani, ta ce:

Kara karanta wannan

Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

“Masarutar Musulunci ta (Afghanistan) ba ta so a kuntata wa mata, muna kira da su shigo gwamnati bisa tsarin Musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel