Buhari ya yi alhinin mutuwar Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa

Buhari ya yi alhinin mutuwar Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna alhini kan mutuwar Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa
  • Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga iyalai, gwamnatin jihar Filato da ‘yan asalin jihar a yayin da suke juyayin rasuwar shahararren dan siyasar
  • Ya kuma yi addu'a kan Allah ya ji kan mamacin

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jajantawa iyalan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu, wanda ya rasu a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, yana da shekaru 74.

Punch ta ruwaito cewa mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 17 ga watan Austa.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Shugaba Buhari ya yi ta’aziyyar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu’.

Buhari ya yi alhinin mutuwar Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa
Buhari ya mika ta'aziyyarsa kan mutuwar Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa na cika da bakin ciki da nadama, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya magantu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Buhari ya jajantawa iyalan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ibrahim Mantu, tare da gwamnatin jihar Filato da ‘yan asalin jihar a yayin da suke juyayin rasuwar shahararren dan siyasar.
"Shugaba Buhari ya yi ta'aziyya ga shugabanni da 'yan Majalisar Tarayya, abokai da abokan siyasar tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ya sadaukar da mafi yawan rayuwarsa ga hidimar mutanensa."

Channels TV ta kuma ruwaito cewa Buhari ya yi addu’a kan Allah ya ji kan mamacin, yana mai cewa koyaushe za a tuna da kokarin Mantu na sulhu da haɓɓaka zaman lafiya, musamman wajen kawo ƙarin jituwa a jiharsa da ƙasa baki ɗaya.

Allah ya yiwa Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa rasuwa

A baya mun kawo cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma Sanata da ya wakilci Plateau ta tsakiya, Ibrahim Nasir Mantu, ya rigamu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Buhari ya koɗa Janar Ibrahim Babangida yayin da ya cika shekara 80 a Duniya

Mantu ya mutu da cikin daren Talata misalin karfe 2.

Wata majiya ta tabbatarwa DailyTrust cewa tsohon dan majalisan ya mutu ne a wani asibiti dake cikin birnin tarayya Abuja bayan kwanaki tara yana jinya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel