Komai ya dawo daidai: Shugaba Buhari zai fito daga kullen Korona ranar Laraba mai zuwa

Komai ya dawo daidai: Shugaba Buhari zai fito daga kullen Korona ranar Laraba mai zuwa

  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, shugaba Buhari zai kammala killacen da ya shiga ranar Laraba mai zuwa
  • Killacen ya biyo bayan dawowa daga Landan, inda shugaban ya kasance na wasu kwanaki na ziyarar aiki
  • Shugaban ya yi ayyukansa daga gida, daga ciki har ya rattaba hannu kan kudurin dokar masana'antar man fetur

Abuja - A ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari zai fito daga killacewar da ya shiga tun bayan dawowarsa daga Landan ranar Juma’a da ta gabata, Nigerian Tribune ta ruwaito.

A bisa ka'ida, dole ne ya killace kansa a matsayin matakin taka tsantsan da ake bukata daga duk matafiya na duniya da ke shigowa Najeriya domin rage yaduwar Korona.

Wasu daga cikin ma’aikatan Babban Kwamishinan Najeriya a Burtaniya wadanda ake tunanin sun kasance tare da shugaban an ce sun kamu da cutar. Amma ba a san ko sun taba kasancewa kusa da shi ba.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Komai ya dawo daidai: Shugaba Buhari zai fito daga kullen Korona ranar Laraba mai zuwa
Shugaba Buhari na Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sai dai, duk da killace da shugaban ya shiga, ya ci gaba da aiki kan takardun gwamnati ciki har da sanya hannu kan dokar Masana'antar Mai (PIB) a ranar Litinin 16 ga watan Agusta.

Ta yaya shugaban yake aiki daga gida?

Fadar shugaban kasa a ranar Litinin ta tabbatar da cewa yana daukar matakai don tabbatar da cewa ya kare kansa yayin duba takardun gwamnati, kamar yadda Sun News ta wallafa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa duk wasu takardu da aka kawo masa an tsabtace su kafin su isa gare shi.

Ya ce:

“Shugaban kasa da gaske yana killace kamar yadda ake bukata bayan tafiye-tafiye na kasa da kasa.
"A cikin wannan lokacin, wanda zai kare ranar Laraba, zai kasance yana duba takardun gaggawa da kuma masu mahimmanci.

Kara karanta wannan

Buhari ga turawan yamma: Ba ma bukatar sojojinku, hannun jari muke bukata

"Yana da mahimmanci a lura cewa duk takardun da ke zuwa ga Shugaban kasa ana bincikar su kuma a tsabtace su tare da kayan aiki na musamman kafin da bayan isa gare shi.
"Dokar PIB da aka rattaba hannu ta wuce ta wannan hanyar."

Buhari ga turawan yamma: Ba ma bukatar sojojinku, hannun jari muke bukata

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kasashen Afrika basa bukatar dandazon sojojin Amurka da sauran dakarun turai don magance matsalolin da suke fuskanta na ta'addanci.

A cewar shugaban, kasashen Afrika na da dakarun da za su iya tunkarar kowane irin yaki ne ba tare da hannun Amurka da wata kasar turai ba, duk da cewa ya amince da kasashen Afrika na bukatar wadatattun kayan aiki.

Shugaban ya bayyana haka ne cikin wata makala da ya wallafa a jaridar Financial Times jiya Lahadi 15 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur

Asali: Legit.ng

Online view pixel