2023: Yemi Osinbajo ya bayyana abin da zai faru da APC bayan Shugaba Buhari ya bar mulki

2023: Yemi Osinbajo ya bayyana abin da zai faru da APC bayan Shugaba Buhari ya bar mulki

  • Tuni jam’iyya mai mulki, All Progressives Congress, ke shirin yadda za ta ci gaba da kasancewa mai tasiri bayan wa’adin mulkin Shugaba Buhari
  • Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya fadawa membobin jam'iyyar abin da ya kamata a yi don samun nasarar jam'iyyar a gaba
  • Babbar jam'iyyar adawa, Peoples Democratic Party, ta riga ta yi alkawarin kayar da APC a babban zaben 2023

Abuja - Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya ba da shawarar cewa farin jinin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na iya samun tangarda a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bar mulki.

Osinbajo a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, ya shaidawa mambobin kungiyar matasa na jam'iyyar APC na kasa cewa yayin da jam'iyyar ke samun farin jini a halin yanzu a karkashin jagorancin shugaban kasa, lamarin na iya sauyawa bayan mulkin Buhari a 2023.

Kara karanta wannan

A karshe jagoran APC, Asiwaju Tinubu ya yi magana, ya gode wa Buhari kan ziyarar da ya kai masa a Landan

2023: Yemi Osinbajo ya bayyana abin da zai faru da APC bayan Shugaba Buhari ya bar mulki
Yemi Osinbajo ya ce barin Buhari mulki a 2023 na iya shafar farin Jinin APC Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito, ya bukaci matasan jam'iyyar da su hada kan matasan Najeriya a fadin kasar don shiga jam'iyyar tun daga matakin unguwa.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa dole ne membobin jam'iyyar su yi aiki tukuru don jawo kuri'u zuwa APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Osinbajo ya ce:

“A yau, APC za ta iya cin zabe, me zai hana, muna da Shugaban kasa mai farin jini wanda zai iya sarrafa manyan kuri’u, muna da abokan hulda a ko’ina.
“Alhalin, a cikin shekaru masu zuwa, lokacin da ba mu da irin wannan jagoran siyasa wanda ya shahara kamar Shugaban ƙasa, za ka buƙaci yin aiki tukuru. Ba za mu iya ɗaukar cewa duk ƙuri'un za su shigo ba.”

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan karfin matasan na iya yin abubuwa a dukkan bangarorin siyasa.

Kara karanta wannan

APC da PDP duk daya ne, in ji tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Doyin Okupe

2023: Fitaccen jigon APC ya bayyana yankin da zai samar da wanda zai gaji Buhari

A wani labarin, Kashim Ibrahim-Imam, jigo a jam'iyyar ya rufe hasashen fitowar dan takarar shugaban kasa na APC daga shiyyar kudu maso kudu da kudu maso gabas.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa dan takarar gwamnan na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sau biyu, wanda a yanzu jigo ne na APC, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, a wani shiri na Arise TV.

Ibrahim-Imam, ya ce jam’iyya mai mulki ba ta da karfi a shiyyar kudu maso kudu da kudu maso gabas, saboda haka ba za ta zabi dan takararta daga shiyyoyi biyun ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel