Da duminsa: Allah ya yiwa Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa rasuwa

Da duminsa: Allah ya yiwa Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa rasuwa

  • Tsohon dan majalisar dattawan tarayya ya mutu
  • Marigayin ya kasance daya daga cikin wadanda suka hana Obasanjo tazarce
  • Manyan masu fada a ji sun yi alhinin rasuwar Ibrahim Mantu

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma Sanata da ya wakilci Plateau ta tsakiya, Ibrahim Nasir Mantu, ya rigamu gidan gaskiya.

Mantu ya mutu da cikin daren Talata misalin karfe 2.

Wata majiya ta tabbatarwa DailyTrust cewa tsohon dan majalisan ya mutu ne a wani asibiti dake cikin birnin tarayya Abuja bayan kwanaki tara yana jinya.

Yace:

"Ya fara rashin lafiya kwanaki tara da suka gabata kuma ya fara jinya a gida amma aka kaishi asibiti."

Ya kara da cewa za'a yi Jana'izarsa a Abuja.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa na cika da bakin ciki da nadama, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya magantu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da duminsa: Allah ya yiwa Suleiman Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa rasuwa
Da duminsa: Allah ya yiwa Suleiman Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa rasuwa
Asali: Original

Buhari ya yi alhinin mutuwar Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jajantawa iyalan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu, wanda ya rasu a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, yana da shekaru 74.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 17 ga watan Austa.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Shugaba Buhari ya yi ta’aziyyar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu’.

Asali: Legit.ng

Online view pixel