Farashin litar man fetur zai iya kai N300 bayan Shugaba Buhari ya sa hannu a dokar PIB

Farashin litar man fetur zai iya kai N300 bayan Shugaba Buhari ya sa hannu a dokar PIB

  • A yau ne Timipre Sylva zai tattauna da manema labarai a kan lamarin PIB
  • Karamin Ministan harkokin fetur na kasa zai bayyana matsayar gwamnati
  • Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta bada sanarwa ta janye tallafin fetur

Abuja - Gwamnatin tarayya na iya daina biyan tallafin man fetur a dalilin sa hannu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a kan kudirin PIB.

Timipre Sylva zai zauna da manema labarai

Punch ta kawo rahoto a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, 2021, cewa Ministan harkokin man fetur, Timipre Sylva zai yi magana a kan wannan batu yau.

Rahotanni suna bayyana cewa ya kamata farashin litar man fetur ya kai har kimanin N300 daga N162 zuwa N165 da ake saida wa yanzu a gidajen mai.

Wani jami’in ma’aikatar man fetur ta kasa, ya shaida wa jaridar cewa karamin Ministan zai yi wa ‘yan jarida bayanin matsayar gwamnati kan tallafin.

Kara karanta wannan

Dalilinmu na daina daukar sababbin ma’aikata a aiki a Gwamnati inji Ministan kwadago

“Watakila ya bada sanarwar sabon matakin da za a dauka game da tallafin da PIB ya cire.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan kasuwa sun ce tun da PIB ya zama doka, sai yadda suka yi da farashin fetur. Billy Gillis-Harry yace tsarin tallafin ya dade yana kawo masu cikas.

Buhari signs PIB
Shugaba Buhari ya sa hannu a dokar PIB Hoto: @NgrPresidency/Facebook
Asali: Facebook

Tun ba yau ba, Timipre Sylva ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta daina biyan tallafin man fetur da zarar an shigo da dokar PIB da aka dade ana jira.

Ya za ayi da NNPC, PPPRA dsr?

Idan aka kyale ‘yan kasuwa su rika tsaida farashi kamar yadda sabuwar dokar ta PIB ta yi tanadi, fetur zai kara kudi, sannan za a yi wa hukumar NNPC dai-daya.

Daily Trust ta ce babu mamaki a soke hukumomin NNPC, PEF, PPPRA a dalilin haka, wanda wannan ya jawo suka da yabo daga bangarori daban-dabam.

Kara karanta wannan

Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno

Wani sauyi da za a samu a kasar shi ne za a rika ware 3% na ribar da aka samu daga saida danyen mai, ga jihohin da ake hako wannan arziki a karkashin kasarsu.

Abin da dokar PIB ta kunsa

A kwanaki kun ji cewa PIB za ta bada damar a saida NNPC, a saida hannun jarin gwamnati da ke kamfanin. NNPC zai koma NNPC Limited a karkashin ‘yan kasuwa.

Haka zalika za a kashe hukumomin Petroleum Equalisation Fund (PEF) da Petroleum Products Pricing Regulatory Agency (PPPRA), a shigo da wasu sababbin haraji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel