Shugaban kasa Buhari ya koɗa Janar Ibrahim Babangida yayin da ya cika shekara 80 a Duniya

Shugaban kasa Buhari ya koɗa Janar Ibrahim Babangida yayin da ya cika shekara 80 a Duniya

  • Muhammadu Buhari ya taya Ibrahim Babangida murnar kara shekara a Duniya
  • Tsohon Shugaban na mulkin soja ya na bikin murnar isa shekara 80 da haihuwa
  • Shugaban Najeriya ya yi jawabi, ya yabi IBB, ya yi masa fata ya kara tsawon rai

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Me Garba Shehu ya fada a jawabinsa?

Mai girma Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi ta bakin babban mai ba shi shawara wajen yada labarai da hulda da jama’a, Malam Garba Shehu.

The Nation ta rahoto Garba Shehu yana cewa shugaba Muhammadu Buhari sun yi tarayya da Ibrahim Babangida wajen ganin kasa ta gyaru.

Buhari ya yi kira ga Babangida da ire-irensa, su dage wajen ganin Najeriya ta yi nasarar kai ga ci.

Kara karanta wannan

Femi Adesina: Abin da ya sa aka ga Buhari ya je har gida ya ziyarci Tinubu kafin ya baro Ingila

“Muhammadu Buhari ya aika sakon taya murnarsa ga tsohon shugaba Ibrahim Babangida, ya na masa afatan tsawon rai yayin da ya ke cika shekara 80.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Shugaban kasa Buhari ya ce a matsayinsu na tsofaffin sojojin yaki da suka yi ritaya, duk sun hadu a wajen fatan alheri da sha’awar ganin an samu hadin-kai a Najeriya.”

Buhari da Babangida
Shugaba Buhari da Janar Ibrahim Babangida Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

“Shugaban kasa Buhari ya na sa ran cewa manyan mutane irinsu tsohon shugaba Babangida da ire-irensa za su taimaka wajen taimakon kasar ga nasara, da cigaba.”

Tsohon soja ya na bikin isa 80

Gidan talabijin na Channels TV ta kawo rahoton jawabin da Garba Shehu ya fitar a madadin shugaban kasa a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, 2021.

Rahoton ya ce Muhammadu Buhari ya shiga cikin sahun masu taya tsohon shugaban kasar na mulkin soja murnar kara shekarar da ya yi a ban kasa.

Kara karanta wannan

A karshe jagoran APC, Asiwaju Tinubu ya yi magana, ya gode wa Buhari kan ziyarar da ya kai masa a Landan

Babangida mai ritaya ya yi mulki na tsawon shekaru takwas tsakanin 1985 da 1993 bayan ya hambarar da gwamnatin Janar Buhari a wancan lokacin.

Dazu kun ji labari daga bakin Femi Otedola cewa Janar Ibrahim Babangida ne ya warware tirka-tirkar da aka shiga lokacin da Ummaru ‘Yaradua yake jinya.

Littafin da Femi Otedola ya rubuta, ya na kunshe da labarin shawarar da Babangida ya ba Attajirin a lokacin da ake neman yadda Jonathan zai karbi mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel