Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur
  • Shugaban ya rattaba hannun ne yayin da yake aiki daga gida saboda zaman killace bayan dawowa daga Landan
  • Dokar za ta samar da tsari da gudanarwa mai kyau ga masana'antar man fetur a Najeriya

Abuja - Rahoton da muke samu daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur.

Legit.ng Hausa ta samo wata sanarwar mai ba shugaba shawari na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, inda ta bayyana rattaba hannun shugaban a yau Litinin 16 ga watan Agusta, 2021.

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan dokar masana'antar man fetur
Shugaba Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Femi Adesina ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:

Kara karanta wannan

Dan majalisar wakilai mai ci a jam'iyyar PDP ya rigamu gidan gaskiya

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur na shekarar 2021 don zama doka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Aiki daga gida cikin keBewa na kwanaki biyar kamar yadda Kwamitin Kula da Shugaban Kasa kan COVID-19 ke bukata bayan dawowarsa daga Landan a ranar Juma'a, 13 ga Agusta, Shugaban ya amince da dokar ranar Litinin, 16 ga Agusta, a cikin kudurinsa na cika aikinsa na tsarin mulki."

Hakazalika, Femi Adesina ya bayyana cewa, za a yi bikin samar da dokar a ranar Laraba mai zuwa bayan shugaban ya fito daga kebe da yake ciki na kwanaki biyar.

Da yake karin bayani game da dokar, Adesina ya ce:

"Dokar Masana'antar Man Fetur za ta samar da doka, shugabanci, tsari da kasafin kudi ga masana'antar man fetur ta Najeriya, ci gaban al'ummomin da ke zaune a yankunan mai, da abubuwan da suka danganci hakan.

Kara karanta wannan

A karshe jagoran APC, Asiwaju Tinubu ya yi magana, ya gode wa Buhari kan ziyarar da ya kai masa a Landan

"Majalisar dattijai ta zartar da kudirin a ranar 15 ga Yuli, 2021, yayin da Majalisar Wakilai ta yi haka a ranar 16 ga Yuli, don haka ya kawo karshen dogon jira tun farkon shekarun 2000, kuma hakan karin girma ne ga gwamnatin Buhari."

Rikici ya barke a zauren majalisa kan batun dokar masana'antar man fetur

Idan baku manta ba a watan Yuli, rikici ya barke a zauren majalisar wakilai a ranar Alhamis kan Dokar Masana’antar Man Fetur (PIB), Daily Trust ta ruwaito.

Rikicin ya fara ne bayan da wasu ‘yan majalisar suka tada jiyoyin wuya kan zargin ragin kaso da aka amince akai ga al’ummomin dake zaune a yankuna masu man fetur.

Majalisar ta riga ta zabi 5% ga al'ummomin dake zaune a yankuna masu man fetur a cikin kudurin PIB a baya yayin da Majalisar Dattawa ta zartar da 3%.

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa take da tsauri kan tafiya kasar waje

Kara karanta wannan

Abinda Shugaba Buhari Zai Fara Yi Bayan Dawowarsa Daga Landan, Femi Adesina

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta ce ta sanya tsauraran ka'idojin balaguro zuwa kasashen waje ne don kare 'yan kasar daga kamuwa da cutar ta Korona, Punch ta ruwaito.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Laraba 11 ga awatan Agusta.

Mohammed ya ce an sanya Najeriya a matsayin kasa mai tsaurin ra'ayi dangane da ka'idojin tafiye-tafiye, yana mai bayanin cewa matsayin gwamnati shi ne kare mutanenta daga yaduwar cutar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel