Shugaban Afghanistan ya tsere daga kasar yayin da Taliban ke dab da shiga Kabul

Shugaban Afghanistan ya tsere daga kasar yayin da Taliban ke dab da shiga Kabul

  • Shugaba Ashraf Ghani na kasar Afghanistan ya tsere daga kasar biyo bayan mamayar Taliban
  • Rahotanni daga kasar na bayyana cewa, a halin yanzu, Kabul na cikin firgici yayin da Taliban ke kara kaimi a lardin
  • Rahoto ya kuma bayyana cewa, shugaban tuni ya tsallaka zuwa Tajiskistan domin tsira da ransa

Afghanistan - A kasashen ketare kuwa, shugaba Ashraf Ghani ya tsere daga Afghanistan yayin da Taliban ke dab da shiga birnin Kabul, a cewar babban mai shiga tsakani na zaman lafiya na kasar Abdullah Abdullah.

Abdullah, shugaban babbar majalisar sasantawa ta kasa, a wani faifan bidiyo a shafinsa na Facebook yana cewa:

"Tsohon shugaban na Afgahnistan ya bar al'umma."

Wani babban jami’in ma’aikatar harkokin cikin gida ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Ghani ya tafi ne zuwa Tajikistan.

Kara karanta wannan

Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno

Ficewar Ghani ta zo ne a yayin tattaunawar mika mulki cikin lumana bayan mayakan Taliban sun kewaye Kabul bayan da suka kwace manyan biranen larduna 34 na kasar cikin kasa da makonni biyu.

Shugaban kasar Afganistan ya tsere daga kasar yayin da Taliban ke dab da shiga Kabul
Ashraf Ghani | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin da ake ciki, wani jami'in Taliban ya shaida wa Reuters cewa suna duba rahotannin ficewar Ghani daga kasar.

A ranar Lahadin da ta gabata, sojojin Taliban sun kewaye fadar mulkin Afghanistan, inda suka yi alkawarin cewa Taliban ta umarci mayakanta da su guji tashin hankali tare da bayar da kariya ga duk wanda ke son barin Kabul.

Kabul na cikin firgici yayin da mayakan Taliban ke kara kaimi

A yayin da kungiyar Taliban ke kara kaimi a Kabul, ana kara samun fargaba a tsakanin mutane da dama a Kabul babban birnin Afghanistan.

Farashin kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi yayin da da yawa ke kokarin cire dukkan kudadensu, in ji rahoton Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

Indonisiya ta yi nadama kan yadda aka ci zarafin jami'in diflomasiyyar Najeriya

A wani labarin daban, Gwamnatin Indonisiya ta bayyana yin nadama da abin da ya faru da jami’in diflomasiyar Najeriya inda wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna jami’anta na shige da fice sun makure shi, BBC Hausa ta ruwaito.

Bidiyon ya nuna yadda jami’in mai suna Abdulrahman Ibrahim wasu maza sun cukuikuye shi a cikin mota.

Najeriya bayan fitar bidiyon ta nuna fushinta tare da yin Allah wadai da abin da ya faru wanda ta ce “ya saba dokar kasa da kasa.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel