Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos

  • Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da kashe musulmai da wasu 'yan ta'addan kiristoci suka yi a Jos
  • Miyetti Allah ya bayyana hakan a matsayin mummunan abu, kuma ya kamata a gaggauta daukar matakin kan lamarin
  • Kungiyar ta kuma yi ta'aziyya da mika jaje ga iyalan wadanda suka rasu da kuma wadanda suka raunata a harin

Jos, Filato - Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu 'yan ta'adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, Punch ta ruwaito.

Wasu 'yan ta'adda a ranar Asabar sun kai hari kan jerin gwanon motocin bas da ke dauke da matafiya musulmai, inda suka kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba.

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi martani kan kisan musulami a Jos
Taswirar jihar Filato | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Baba Othman ya ce:

“Harin na kwanton baunar da ya faru da misalin karfe 10:00 na safe, ya kuma raunata matafiya da dama, yayin da wasu 40 kuma ba a ji duriyarsu ba.
“Matafiyan suna cikin ayarin motocin bas guda hudu, lokacin da aka kai musu hari.
"Miyetti Allah ta yi Allah wadai da wannan tashin hankali mara ma'ana akan matafiya.
"Muna kira ga hukumomin tsaro da su zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aikin kuma su gurfanar da su a gaban kuliya."

Ngelzarma ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata.

Kara karanta wannan

A tura 'yan Boko Haram da suka tuba zuwa gonaki, tsohon Janar ya shawarci FG

Ya ce ba za a iya samun wanda ya yi nasara ba a tashin hankalin da ba shi da ma'ana kuma dole ne a dakatar da zub da jini.

Kisan Gillan Musulmi a Jos: Kungiyar Kare Hakkin Musulmai MURIC Ta Yi Kira a Kame Kiristocin Irigwe

Kungiyar fafutukar kare hakkin musulmai (MURIC) ta yi kira da a gaggauta kame gaba daya wadanda suka aikata kisan musulmai matafiya a Jos, inda ta kira su da "Mayakan kiristoci a Jos."

Daily Nigerian ta ruwaito cewa matafiya musulmai 25 wasu sojojin kungiyar kiristanci suka kashe a Rukaba, jihar Filato ranar Asabar.

A wani jawabi da daraktan MURIC, Ishaq Akintola, ya fitar, ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa musulmai, tare da kira ga gwamnati ta kame waɗanda suka aikata kisan.

An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

A baya, rundunar tsaro ta musamman, Operation Safe Haven (OPSH) a jihar Filato, ta cafke wasu mutane 12 da ake zargi da aikata kashe-kashe da safiyar Asabar a kan hanyar Rukuba ta karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar, in ji rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

A sabbin rahotanni da suka shigo a yau kuwa, Daily Trust ta ruwaito cewa, mutane 20 ne ya zuwa yanzu a cafke da hannu wajen kisan musulmai 25 a wani yankin jihar Filato.

Manjo Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na rundunar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ranar Asabar a garin Jos.

Asali: Legit.ng

Online view pixel