Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyuka Sun Kashe Mutane da Dama Tare da Sace Wasu a Sokoto

Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyuka Sun Kashe Mutane da Dama Tare da Sace Wasu a Sokoto

  • Wasu yan bindiga sun hallaka mutane tare da jikkata wasu a kauyuka uku dake jihar Sokoto
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun mamayi Benjigo, Dantudu da Tulutu dake karamar hukumar Goronyo ranar Asabar
  • Jihar Sokoto dake cikin yankin arewa maso gabas na fama da harin yan bindiga da kuma satar mutane domin neman kuɗin fansa

Sokoto - Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 9 tare da sace wasu shida a wani hari da suka kai kauyukan karamar hukumar Goronyo, jihar Sokoto, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Channels tv ta ruwaito cewa harin ya shafi ƙauyuka uku da suka hada da, Bejingo, Dantudu da kuma Tulutu.

Wata majiya daga yankin wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa maharan sun kashe maza 8 tare da wata mace ɗaya ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yadda Wasu Fusatattu Mutanen Gari Suka Tari Yan Bindiga, Suka Hallaka Daya Daga Ciki a Taraba

Yace: "Maharan sun kashe maza 8 da kuma wata mace ɗaya, yayin da suka jikkata wasu da dama."

Yan bindiga sun kai hari kauyuka a Sokoto
Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyuka Sun Kashe Mutane da Dama Tare da Sace Wasu a Sokoto Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Maharan sun yi awon gaba da dabbobi

Hakazalika rahoto ya nuna cewa yan bindiga sun yi awon gaba da dabbobi masu yawa waɗanda ba'a san iyakar adadin su ba.

Mutanen dake zaune a kauyukan sun fara ficewa zuwa makotansu domin tseratar da rayuwarsu daga yan bindigan.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka

Har yanzun hukumar yan sanda bata ce komai ba game da lamarin domin kakakin hukumar ta jihar, Muhammad Sadiq, yace babu wani rahoto da suka samu kan harin.

An yiwa gawarwakin waɗanda aka kashe jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya koyar.

Sokoto, na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammacin ƙasar nan da matsalar taro ta shafa, inda take fuskantar harin yan bindiga da kuma satar mutane domin neman kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Matasan mayakan Boko Haram 14, mata da yara 31 sun sake mika wuya a Konduga

A watan da ya gabata, yan bindiga sun kashe mutum 2 tare da sace matafiya sama da 60 a kan babbar hanyar Sokoto-Gusau.

A wani labarin kuma Sojoji Sun Ceto Karin Mutum 7 Daga Cikin Musulman da Aka Kaiwa Hari a Jos

Sojojin Najeriya a jihar Filato na Opertaion Safe Haven sun bayyana cewa sun ceto ƙarin mutum 7 daga cikin waɗanda harin Jos ya rutsa da su.

Wannan na zuwa ne bayan wani hari da aka kaiwa matafiya a kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta arewa , jihar Filato.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel