Sanusi II: Najeriya ba ta cimma komai ba cikin shekaru 40, dole na fadi gaskiya

Sanusi II: Najeriya ba ta cimma komai ba cikin shekaru 40, dole na fadi gaskiya

  • Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana yadda Najeriya ta gagara cimma komai cikin shekaru 40
  • A cewarsa, maganganun da yake a baya, an dauka yana sukar lamirin abubuwan da ke faruwa ne, amma yanzu ga gaskiyar batu
  • Ya kuma roki 'yan Najeriya da a tashi tsaye wajen ganin an inganta tattalin arzikin kasar nan ba babba ba yaro

Kaduna - Alhaji Muhammad Sanusi, tsohon Sarkin Kano, ya ce Najeriya ba ta samu wani ci gaba ba cikin shekaru 40, tun mulkin shugaban kasa Shagari, Daily Trust ta ruwaito.

Sanusi ya fadi haka ne a wani taron tattaunawa na murnar cikarsa shekaru 60 a duniya da aka gabatar jiya Asabar 14 ga watan Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Kuyi hakuri da gwamnatin Buhari, Minista yayi kira matasa marasa aiki

Tsohon Gwamnan na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce akwai bukatar ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa.

Najeriya bata cimma komai ba cikin shekaru 40, in ji Muhammadu Sanusi II
Tsohon sarkin Kano Sanusi | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Na biya farashin fadin gaskiya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce duk da ya biya farashi saboda fadin gaskiya, ‘yan Najeriya sune suka biya ainihin farashi ta bangaren zama “cikin talauci, rashin tsaro, da hauhawar farashin kaya ”.

A cewarsa:

"Lokacin da kuke cikin al'ummar da ba daidai take ba, ba za ki iya zama mai daidaita abubuwa ba, saboda idan duk kun daidaita, abubuwa ba za su canza ba."
“Shekaru da yawa da suka gabata, lokacin da nake kururuwa akan biliyoyin da ake kashewa akan tallafin man fetur, na tuna an yi yunkurin kai hari gidana a Kano. Sannan ina CBN. Ina muke a yau? Muna fuskantar gaskiya - cewa tallafin mai ba zai dawwama ba.

Dole ne mu fuskanci gaskiya

Kara karanta wannan

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

Legit Hausa ta tattaro daga rahoton Daily Trust cewa, Sanusi ya kara da jan hankali cewa:

"Kira na makiyi ko mai sukar lamiri ba zai sa wadannan hujjojin su tafi ba. Don haka, duk inda muka je, dole ne mu fuskanci wannan gaskiyar.
"Na yi kokarin kada in fadi da yawa, ba wai saboda babu abin da zan fadi ko saboda ina jin tsoron magana ba.
"Dalilin da yasa ban yi magana da yawa ba a cikin shekaru biyu da suka gabata shine saboda, ba ma sai na sake cewa komai ba, saboda duk abubuwan da muke gargadin su sun bayyana.
“A cewar Bankin Duniya, ina muke a 2019? A wannan adadin, a cikin shekaru biyu masu zuwa, dangane da daidaiton ikon siye, matsakaicin kudin shiga na dan Najeriya zai koma yadda yake a da tun 1980 a karkashin mulkin Shehu Shagari.
"Wannan yana nufin a cikin shekaru 40, ba mu sami ci gaba ba; Shekaru 40 sun lalace a banza.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

“Muna da nauyi a matsayin mu na mutane, mu tashi mu inganta rayuwar mutanen kasar nan. Idan gobara ta tashi, kowa ya tafi da likidiri don debo ruwan kashe ta. Muna bukatar fahimtar yadda tattalin arzikin mu ke aiki a matsayinmu na mutane; muna bukatar fahimtar zabin mu.
“Ko da wannan ihun game da sake fasalin ya shafi tattalin arziki; yana magana ne game da albarkatu. Muna bukatar habaka tattalin arzikin da sanya shi aiki ga talakawa.”

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto; tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Kingsley Moghalu; mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe; Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamali; duk sun halarci taron tattaunawar.

Abokin kirki: El-Rufa'i ya tuna yadda ya hadu da tsohon sarkin Kano Sanusi a jami'a

A wani labarin, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya jinjinawa tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, inda ya bayyana shi a matsayin babban abokin da kowa ya kamata ya samu, DailyTrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Ba a ga daman ceto yaran da ake sace wa bane inji Tsohon Ministan Buhari

Da yake magana a taron maulidin shekara-shekara na Muhammadu Sanusi II a Kaduna, El-Rufai, wanda ya yi magana ta yanar gizo kasancewar yana kasar waje, ya ba da labarin yadda su biyun suka hadu a matsayin dalibai a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Ya ce a wancan lokacin, tsohon sarkin Kano ya fito fili wajen fadin ra’ayoyinsa kuma ya bayyana hangoronsa da burinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel