Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

  • Rundunar sojojin Najeriya a jihar Filato sun cafke wasu mutune 20 da ake zargi da kashe matafiya musulmai
  • Wannan ya zo ne bayan da wasu 'yan ta'adda suka yi wa matafiya kisan gilla a wani yankin jihar ta Filato
  • A halin yanzu, rundunar ta ce tana kan bincike don tabbatar da adalci da kuma mika su ga inda ya dace

Jos, Filato - A baya, rundunar tsaro ta musamman, Operation Safe Haven (OPSH) a jihar Filato, ta cafke wasu mutane 12 da ake zargi da aikata kashe-kashe da safiyar Asabar a kan hanyar Rukuba ta karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar, in ji rahoton PM News.

A sabbin rahotanni da suka shigo a yau kuwa, Daily Trust ta ruwaito cewa, mutane 20 ne ya zuwa yanzu a cafke da hannu wajen kisan musulmai 25 a wani yankin jihar Filato.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayin da ‘yan bindiga suka bude wuta kan matafiya a Jos

Manjo Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na rundunar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ranar Asabar a garin Jos.

Sojoji sun cafke mutum 12 da ake zargi da kisan musulmai a Jos
Gawarwakin Mutanen da aka kashe | Hoto: Ado Abubakar Musa
Asali: Facebook

Wani yankin sanarwar ya shaida cewa:

"Wadanda aka kama a halin yanzu suna tsare don amsa tambayoyi."

Takwa ya ce Kwamandan rundunar, Maj-Gen. Ibrahim Ali, ya bukaci jama'a da su ba da sahihan bayanai masu sahihanci wadanda za su kai ga cafke sauran wadanda ake zargi, a halin yanzu.

Ya ce, kwamandan ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka da oda kuma su ci gaba da ayyukansu ba tare da wani fargaba ba.

Hakazalika, ya ce jami'an tsaro sun kara kaimi wajen sintiri a cikin garin Jos don wanzar da zaman lafiya da tsaro.

An yi jana'izar Musulmai 25 da matasan Irigwe suka kashe a garin Jos yau Asabar

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

An yi jana'izar matasan da halarci taron Zikirin kasa a jihar Bauchi 25 da yan bindigan kabilar Irigwe suka hallaka a Gada-biyu, karamar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Plateau.

An bizne mamatan ne a makabartar Dadinkowa da cikin jihar, rahoton Daily Nigerian. Jami'in gwamnatin mai suna Danladi Atu wanda ya ziyarci asibitin da aka kai wadanda suka jikkata yace mutum 25 aka tabbatar yanzu sun mutu.

Hakazalika kungiyar Miyetti Allah MACBAN tace ta kirga gawawwaki 25. Wakilin Miyetti Allah, Malam Nura Abdullahi yace: "Mun yiwa gawawwaki 25 wanka kuma muna shirin biznesu."

Sojojin Najeriya za su yi wa tubabbun 'yan ta'adda karatun gyaran hali

A wani labarin, Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta karba tare da aiwatar da karatun gyaran hali ga 'yan ta'adda da suka mika wuya kafin mika su ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi martani yayin da matar marigayin kanal ta yi ikirarin cewa kashe mijinta aka yi

Kakakin rundunar, Brig-Gen. Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan ne bayan rahotannin da ke cewa rundunar ta yi karatun gyaran hali tare da sakin wasu kwararrun 'yan ta'adda guda biyu masu kirkirar bam.

“An jawo hankalin mu ga rahoton da wasu kafofin watsa labarai na yanar gizo suka buga wanda marubutan da gangan suka jirkita gaskiyar da ke cikin wannan rahoton kuma suka karkatar da shi don dacewa da duk wata manufar da suke son cimmawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel