Yan sanda sun tabbatar da kisan mutum 22 a Jos, sun ce ana zargin matasan Irigwe ne

Yan sanda sun tabbatar da kisan mutum 22 a Jos, sun ce ana zargin matasan Irigwe ne

  • Kakakin yan sanda Jos yace ana zargin matasan Irigwe (yawancinsu Kirista) suka kaiwa Musulmai 90 hari
  • Jami'in dan sandan ya ce an damke mutum shida cikin maharan
  • Akalla mutum 25 suka mutu yanzu, cewar gwamnatin jihar da Miyetti Allah

Wasu yan bindiga da ake zargin matasan Irigwe ne sun kai wa Musulmai matafiya 90 hari a jihar Plateau ranar Asabar, akalla mutum 22 sun mutu, yan sanda suka tabbatar.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ubah Ogaba, ya bayyana cewa wasu matasa Kirista yan garin Irigwe suka kaiwa Musulman farmaki, rahoton Channelstv.

A cewarsa:

"Misalin karfe 0928hrs, hukumar yan sandan jihar Pleatuea ta samu labarin cewa wasu mahara da ake zargin matasan Irigwe ne (yawancinsu Kirista) sun kai hari kan motocin Musulmai biyar dake hanyar dawowa da taron Zikirin kasa a Bauchi kuma suka nufi Ikare a jihar Ondo."

Kara karanta wannan

Sunayen Matafiya fiye da 20 da aka yi wa kisan gilla a Jos, wani ya rasa 'yanuwansa 7

"Mutum ashirin da biyu aka kashe yayinda 14 suka jikkata."

Jami'in yan sandan ya kara da cewa mutum 21 sun tsallake rijiya da baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan sanda sun tabbatar da kisan mutum 22 a Jos, sun ce ana zargin matasan Irigwe ne
Yan sanda sun tabbatar da kisan mutum 22 a Jos, sun ce ana zargin matasan Irigwe ne Hoto: Governor Simon Lalong
Asali: UGC

Wani jami'in gwamnatin jihar ya bayyanawa Channels cewa adadin wadanda aka kashe ya fi haka.

Jami'in gwamnatin mai suna Danladi Atu wanda ya ziyarci asibitin da aka kai wadanda suka jikkata yace:

"Mutum 25 aka tabbatar yanzu sun mutum."

Hakazalika kungiyar Miyetti Allah MACBAN tace ta kirga gawawwaki 25.

Wakilin Miyetti Allah, Malam Nura Abdullahi yace:

"Mun yiwa gawawwaki 25 wanka kuma muna shirin biznesu."

Gwamnan Plateau, Simon Lalong, ya yi Alla-wadai da wannan hari.

A cewar mai magana da yawunsa, Makut Simon Macham, yace:

"An tura jami'in tsaro wajen."

Hukumar yan sanda yace an damke mutum shida an an kwatar da kuran.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Asali: Legit.ng

Online view pixel