Gwamna Masari ya yi barazanar maka hukumar Kwastam a kotu kan kashe-kashe a Katsina

Gwamna Masari ya yi barazanar maka hukumar Kwastam a kotu kan kashe-kashe a Katsina

  • Gwamnan Katsina, Bello Masari, ya caccaki hukumar kwastam ta Najeriya kan kashe-kashen da akeyi a jihar
  • Gwamnan ya ce zai zama bai da wani zaɓi face ya ja hukumar Kwastam zuwa kotu idan ba a daina kisan ba
  • A cewarsa, gwamnatinsa ba za ta sake yarda da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da hukumar kwastam ke yi

Katsina, Katsina - Biyo bayan kisan da aka yi wa mazauna garin guda 10 yayin aikin atisaye kan iyaka a yankin Jibia na jihar Katsina, Gwamna Aminu Bello Masari, ya yi barazanar daukar matakin shari'a kan hukumar kwastam ta Najeriya (NCS).

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Masari, a cikin wata sanarwa daga babban daraktan yada labaransa, Abdulabaran Malumfashi, yayi Allah wadai da yawan kashe-kashen mazauna jihar da hukumar NCS ke yi.

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

Gwamna Masari ya yi barazanar maaka hukumar Kwastam a kotu kan kashe-kashe a Katsina
Gwamna Bello Masari na shirin maka hukumar kwastam a kotu Hoto: Bello Masari.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Masari ya bayyana cewa daga yanzu gwamnatinsa ba za ta sake lamunta da irin wannan lamari ba.

Ba za a lamunci kashe-kashen mutane da basu ji ba basu gani ba a Katsina

Sanarwar ta ce:

“Gwamnan ya yi Allah-wadai da kashe-kashen rashin hankali da ake yi wa ‘yan kasa ta hanyar tukin ganganci daga jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya.
“Gwamnati na duba yiwuwar daukar matakin doka a kan Hukumar Kwastam ta Najeriya domin hana aukuwar wadannan munanan abubuwan da ke faruwa a cikin jihar.''

Jaridar Premium Times ta kuma ruwaito cewa matsayin Masari ya samo asali ne daga kisan mutane takwas da aka yi kwanan nan, wanda ya haura zuwa 10, wanda jami’an kwastam da ke atisayen kan iyaka a karamar hukumar Jibia suka bi ta kansu a ranar Litinin, 9 ga Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya ba Jihohi shawarar yadda za ayi maganin ta'adin ‘Yan bindiga cikin sauki

Sai dai, gwamnan ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta nade hannu ba yayin da jami'an gwamnati ke kashe 'yan kasa masu bin doka da oda da ya kamata su kare.

Kullum sai an kai hari kananan hukumomin Katsina 10, Aminu Bello Masari

A wani labari na daban, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari yace kananan hukumomi 10 cikin 34 na jihar na fuskantar munanan hare-hare kulli yaumin daga wajen yan bindiga.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin babban hafson soji, Lt Janar Faruk Yahaya, a ranar Alhamis, rahoton DN.

Ya bayyanawa Faruk Yahya cewa yan bindiga na sace mutane, suna jikkata wasu, suna kona gidaje, su yiwa mata fyade kuma su kora Shanu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel