Dan Arewa kadai zai iya ciwa PDP zaben shugaban kasa a 2023, Mai gidan talabijin na AIT

Dan Arewa kadai zai iya ciwa PDP zaben shugaban kasa a 2023, Mai gidan talabijin na AIT

  • Babban jigon PDP ya bayyanawa jam'iyyarsa abinda zatayi idan tana son nasara a 2023
  • Dokpesi wanda ya nemi kujerar shugaban jam'iyyar a baya, yace gwanda su daina yaudarar kansu
  • Yace PDP ta daina kokarin kwafan jam'iyyar APC

Abuja - Babban jigon Peoples Democratic Party (PDP), kuma mammalakin gidan talabijin AIT, Raymond Dokpesi, yace PDP za ta iya cin zaben 2023 ne kawai idan ta fito da dan takara daga Arewa.

A hirar da yayi da jaridar Daily Independent, Dokpesi yace mambobin PDP dake cewa a baiwa dan kudu tikitin kujerar shugaban kasa na yi kawai don kwaikwayon APC ne.

Ya ce babu yadda za'ayi jam'iyyarsa ta PDP ta ci zaben shugaban kasa a 2023 idan ta gabatar da dan takara daga kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen jigon PDP ya bayyana abin da zai yi idan Tinubu ya zama shugaban kasa

Yace:

"Dukkanmu yan Najeriya ne kuma babu amfanin yaudarar kansu yanzu. A shekara 70 da kuma kwarewar da na samu wajen yakin neman zabe a kasar nan. ina tabbatar muku da cewa idan ba'a baiwa dan Arewa tikitin PDP ba, babu yadda za'a ci zabe."
"Game da wadanda ke kudu suna kira ga a baiwa yan kudu tikiti, kawai suna kwaikwayo APC ne. A APC, Shugaba Muhammadu Buhari yayi shekaru takwas, saboda haka akwai bukatar ta mika shugabancin kasa kudu."

Da Arewa kadai zai iya ciwa PDP zaben shugaban kasa a 2023
Da Arewa kadai zai iya ciwa PDP zaben shugaban kasa a 2023, Mai gidan talabijin na AIT Hoto: PDP
Asali: Getty Images

Yan kudu sun fi na Arewa dadewa a kujerar shugaban kasa

A cewarsa dan Arewa daya kacal, Umaru Yar'adua, ya yi mulki karkashin shekarar PDP. Amma na kudu sun yi shekaru 14.

"Amma PDP, mu duba. Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo daga kudu maso yamma yayi shekara takwas; Goodluck Jonathan daga Kudu yayi shekara shida. Ka ga shekaru 14 kenan."

Kara karanta wannan

A bari yan kabilar Igbo su balle kawai mu huta, Tsohon Jakadan Najeriya

"Amma Umaru Yar'adua daga Arewa yayi shekara 3, ka ga akwai banbancin shekaru 11 kenan."
"Saboda haka, idan PDP na son nasara, dan takaran shugaban kasa yazo daga Arewa a 2023. Mutane suyi hakuri saboda komin daren dadewa zai dawo kudu."

PDP ta nemi kotu ta tsige Buni a matsayin gwamnan Yobe

An gurfanar da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a kotu kan nadinsa a matsayin shugaban kwamitin riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, ta shigar da kara na neman a cire Buni daga mukaminsa na gwamnan Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel