Sanatan Borno ya ja-kunnen Sojoji a kan maida tsofaffin ‘Yan ta’addan Boko Haram ‘yan lele

Sanatan Borno ya ja-kunnen Sojoji a kan maida tsofaffin ‘Yan ta’addan Boko Haram ‘yan lele

  • Ali Muhammad Ndume ya jinjina wa irin kokarin da Sojojin Najeriya ke yi
  • Sanatan yace dama ya san rashin kayan aiki ne ya hana Sojojin kasan kokari
  • Ndume ya ja-kunnen jami’an tsaro a kan tarairayar tubabbun Boko Haram

Abuja - Ali Muhammad Ndume, Sanata mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawa, ya yi kira ga jami’an tsaro su kawo karshen ta’addanci a Najeriya.

The Cable ta ce Sanatan na APC ya yabi sojojin Najeriya, sannan kuma ya nemi ayi maza ayi maganin masu tada kafar baya a yankin Arewa maso gabas.

Me ya hana Sojojinmu kokari a baya?

Sanata Ali Muhammad Ndume ya bayyana hakan a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Ba a ga daman ceto yaran da ake sace wa bane inji Tsohon Ministan Buhari

Ali Muhammad Ndume yake cewa nasarorin da sojojin Najeriya suke samu a ‘yan kwanakin nan ya nuna idan akwai kayan yaki, za ayi galaba kan Boko Haram.

Me ya dace da Sojojin Boko Haram da suka tuba?

‘Dan majalisar dattawan ya gargadi sojoji cewa su yi hattara sosai da ‘yan ta’addan da suke mika kansu, yace ya kamata a binciki tsofaffin mayakan a tsanake.

Sanata Ndume ya ja-kunnen jami’an tsaron Najeriya cewa ka da su yi wasa da tubabbun ‘yan ta’addan, ya ce a fara maida hankali kan halin al’ummar yankin.

Sanatan Borno ta Kudu
Sanata Ali Ndume Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Abin bai ba ni mamaki ba dama, saboda na dade ina fada, sojoji da sauran jami’an tsaro ba su da kayan aiki a hannu, amma ba don haka ba, da sun gama yakin nan.”

Kara karanta wannan

Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai

“Yanzu da aka mika masu abubuwan da suke bukata, ku na ganin nasarorin da ake samu a gajeren lokaci. Kuma ina sa ran suyi abin da ya fi wannan.”
“Kamar yadda na fada ne a baya, ka da a bude kofar yin afuwa a wangale, a rika shagwaba wadanda suka mika wuya. Ka da ayi garaje, a bincike su da kyau.”

Abu na farko da ya kamata ayi,, a cewar Ndume shi ne a fara kula da Bayin Allah da ‘yan ta’addan suka jikkata, sai a fara maganar karbar tuban sojojin Boko Haram.

‘Yan Boko Haram suna mika wuya da kansu

Ku na da labari cewa Mayakan kungiyar Boko Haram suna ajiye makamansu a sakamakon hare-haren da ake yawan kai masu. A rana daya an mayaka 49 da iyalansu.

A sakamakon cigaba da bude wa ‘yan Boko Haram wuta da rundunar sojojin Operation Hadin Kai suke ta yi, wasu ‘yan ta’addan Boko Haram da-dama sun sare, sun ajiye kayan yaki.

Kara karanta wannan

Ku kai yakin har zuwa mafakar makiya, COAS, Janar Yahaya ya umarci sojoji

Asali: Legit.ng

Online view pixel