EFCC ta cafke yaro da mahaifiyarsa wacce ya tsoma a harkar damfara ta yanar gizo

EFCC ta cafke yaro da mahaifiyarsa wacce ya tsoma a harkar damfara ta yanar gizo

  • Wasu 'yan damfara sun shiga hannun hukuma bayan da suka aikata munanan laifuka
  • An gano yadda wani matashi ya shigar da mahaifiyarsa harkar damfara ta yanar gizo
  • Hakazalika, an gano wata daga cikin 'yan damfarar da ta sayar da asusun ta na Facebook saboda aikata barna

Kaduna - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) a shiyyar Kaduna ta cafke wasu mutane hudu da suka hada da Lucky Ebhogie, Richman Kas Godwin, Israel Justin da Precious Iwuji da aikata laifin zambar ta yanar gizo.

An damke su ne a ranar 5 ga Agusta, 2021, a unguwar Sabo da ke Kaduna, a Jihar Kaduna biyo bayan bayanan sirri kan zarginsu da hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo, Daily Nigerian ta ruwaito.

Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin galibi suna da hannu cikin aikata zamba da kulla soyayyar karya soyayya; yin karya da sunan ma'aikatan sojin Amurka akan ayyukan kasashen waje don yaudarar mutanen da suka fada fatsarsu.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan shirin sakin manyan kwararrun masu hada bama-bamai na Boko Haram

EFCC ta cafke yaro da mahaifiyarsa wacce ya tsoma a harkar damfara ta yanar gizo
Jami'an EFCC | Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Daya daga cikin wadanda ake tuhuma, Lucky Ebhogie ana zargin ya tsoma mahaifiyarsa, Margaret Sylvester, cikin damfarar ta hanyar amfani da asusunta don aikata laifi.

A ranar 30 ga Yuli, 2021, ya sayi mota kirar Mercedes Benz GLK akan kudi Naira miliyan 7 ta asusun bankin mahaifiyar tasa.

Wata wacce ake zargi, Precious Iwuji an gano cewa ta sayar da hotunan ta da asusun ta na Facebook ga masu damfara ta yanar gizo, wanda suke amfani da shi wajen dasa tarko kan jama'a.

Nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargi zuwa kotu.

Ma'aikatan banki sun hadu da fushin doka bayan sun sace kudin mamaci a bankinsu

Hukumar EFCC, na yankin Uyo, ta tabbatar da hukunta wasu jami'an bankin guda biyu, Daniel Akpan Eno da Mbuk Idongesit, a gaban mai shari'a Edem Ita Kufre na babbar kotun jihar Cross River, Calabar saboda hadin baki da satar kudi a asusun wani abokin cinikinsu da ya mutu.

Kara karanta wannan

Mutane 10 sun jikkata yayin da sojoji suka dakile wani kazamin rikici a Filato

An yanke wa mutanen biyun hukuncin ne a ranar Laraba 4 ga Agusta, 2021 bayan sun amsa laifin da ke da alaka da hadin baki na aikata laifi da zamba, a cewar Daily Nigerian.

Wanda ake tuhuma na uku, kuma wanda ake zargi da hannu a barnar, Victor John Okon ba a kama shi da laifi ba. An daga shari’arsa zuwa ranar 10 ga watan Agusta, 2021 domin duba bukatar ba da belinsa.

Ofishin Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari

A wani labarin, Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, kuma ministan Shari'a Abubakar Malami, ta ce har yanzu ba ta karbi wata takarda a hukumance daga cibiyar binciken Amurka ta FBI ba da ke neman damar kame mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari.

Wannan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga ministan, Umar Gwandu yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tankar mai ta fadi, ta nike mutane da dama a Ibadan

FBI ta zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi, wani dan damfara dake fuskantar zaman kotu a Amurka, bayan kame masa wani abokin harkallarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel